Connect with us

LABARAI

Jihar Kano Ta Kaddamar Da Shirin Samar Da Ruwa Na Shekaru Biyar Kan Naira Bilyan 98

Published

on


Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani shirin samar da ruwa na shekaru biyar wanda za ci kudi sama da Naira bilyan 98.

Kwamishinan albarkatun ruwa na Jihar, Alhaji Usman Riruwai, ne ya kaddamar da shirin wajen wani taro a ranar Talata a Kano, ya ce an kaddamar da shirin ne domin magance matsalar ruwan da ya ki ci-ya ki cinyewa a yankunan karkaran Jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ya hakaito cewa, taron gwamnatin Jihar ne ta shirya shi domin bikin ranar Dimokuradiyya.

Riruwai, ya bayyana cewa, shirin wanda wasu hadakan masu zuba jari daga waje gami da gwamnatin Jiha da kuma ta tarraya ne za su dauki nauyinsa.

Kwamishinan ya ce, gwamnatin Jihar za ta zuba Naira bilyan 25 a kan aikin, Bankin Musulunci kuma zai zuba Naira bilyan 45, sai hukumar, ‘French Debelopment Agency,’ ta kasar Faransa da za ta zuba Naira bilyan 27, kungiyar kasashen Turai kuma za su zuba Naira Bilyan 21.

Sauran masu bayar da gudummawar sun hada da, gwamnatin tarayya wacce za ta bayar da Naira bilyan 3.5, UNICEF, Naira bilyan 1.5, sai hukumar DFID wacce za ta bayar da Naira bilyan guda.

Tun da farko, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Hafiz Abubakar, ya ce Jihar tana da sama da daliban makaranta milyan uku, 6,000 duk su na Firamare ne.

Kwamishinan wanda har ila yau shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar, ya ce Jihar ce ke da mafi yawan dalibai a tsakankanin Jihohin kasarnan.

Ya ce, sama da malamai 2,000 ne Jihar ta dauki nauyin su domin daukan jarabawar NCE domin a inganta ilimi a Jihar.

Hakanan, Kwamishinan raya karkara, Musa Kwankwaso ya ce, gwamnatin Jihar tana aiki tare da Bankin Duniya domin gina hanyoyi masu tsawon Kilomita 500 na karkara a duk sassan Jihar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai