Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Bauchi Ta Zaftare Wa Ma’aikatanta Albashi

Published

on


Kawo yanzu, ma’aikatan gwamnatin Jihar Bauchi sun fara kokawa a bisa zaftare musu wani kaso daga cikin albashinsu na watan Mayu da gwamnatin jihar ta yi.

Wakilinmu ya labarto cewar ma’aikatan gwamnatin sun samu zaftarewar ne a cikin albashinsu na watan Mayu wato watan biyar, inda mafiya yawan ma’aikatan gwamnatin suka wayi gari da kallon albashinsu a rage, bincike ya gano cewar babu wani takamaiman adadi da aka cire wa ma’aikatan, kuma ba an bi girman matsayin aiki ne wajen zarewar ba.

Wakilin mu ya kuma binciko cewar wasu an cire musu dubu 10, wasu 20 wasu 30 har ma da wadanda aka zaftare musu abun da ya dara wa hakan ba tare da sanin dalilin hakan ba.

Wani ma’aikatan fannin shari’a da ya bukaci mu sakaye sunansa ya shaida mana cewar “Ina aiki a karkashin ma’aikatan shari’a, ina kuma aiki ne a babban kotun jihar Bauchi, ni an zaftare min naira dubu goma sha daya 11 daga cikin albashina na watan Mayu,” Kamar yadda ya shaida.

Shi ma wani Darakta da ya boye mana sunansa ya ce; “Ni ina matsayin Darakta ne a karkashin gwamnatin jihar Bauchi, kawo yanzu an zaftare min naira dubu 70 a cikin albashina watan Mayu ba tare da na san dalilin hakan ba,” In ji ma’aikacin mai mukamin Darakta.

Wakilinmu ya shaida mana cewar haka lamarin ya kasance da mafiya yawan ma’aikatan jihar ta Bauchi, sai dai kuma mun gano cewar ba dukkanin ma’aikatan ba ne wannan matsalar ta shafa.

A bisa wannan matsalar da ta karade ma’aikatu da sashi-sashi na ma’aikatan gwamnantin jihar Bauchi, tuni wasu kungiyoyin sashi-sashi suka fara daukan matakai domin ganin sun kwato hakkokinsu daga hanun gwamnatin jihar.

A bisa wannan dalilin ne kungiyar ma’aikatan shari’a wato ‘Judiciary Staff Union of Nigeria’ wato (JUSUN)  reshen jihar Bauchi ta aike da sanarwar gargadi wa dukkanin wadanda abun ya shafa ko kuma su tafi yajin aikin.

Sanarwar wacce aka mammanta a allunan sanarwa da ke cikin babban kotun jihar Bauchi dauke da sanya hanun shugaban kungiyar ta JUSUN a jihar Bauchi Kwamared Adamu B. Ahmed esk wacce kuma aka aike da kwafinta wa dukkanin masu ruwa da tsaki a jihar ta Bauchi.

Kungiyar ta JUSUN ta tunatar da gwamnatin jihar Bauchi kan ababen da suka shafi ‘ya’yan kungiyar kai tsaye domin ganin ba a samu wata babban matsalar da za ta kaisu ga tafiya yajin aiki a sakamakon zaftare musu albashinsu ba.

A bisa wannan dalilin ne manema labaru suka tuntubi shugaban ma’aikatan Bauchi, Alhaji Liman Bello inda ya jinjina ne wa gwamnatin jihar Bauchi a bisa fidda sabon tsarin tattara bayan ma’aikatan jihar wato Bauchi ‘Human Resources Management Information System’ a turance.

Liman Bello ya yi wannan jinjinar ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a ofishinsa da ke  Bauchi, shugaban ma’aikatan ya bayyana cewar HRMIS ya taimaka wajen gano masu amsar albashi sau biyu a jihar.

Dangane da wadanda aka yanke musu hade da zaftare musu albashinsu kuwa, ya bayyana cewar dukkanin wani ma’aikacin da ke da korafi akan albashinsa da cewar ya aike da sunansa da korafinsa ga jami’in da aka daura wa alhakin hakan a ofishinsa.

Ya bayyana cewar sun fidda tsarin ne domin tsaftace aikin gwamnati a jihar ta Bauchi.

A nata janibin kuma, kungiyar kwadago ta jihar NLC reshen jihar Bauchi ta bayyana matukar kaduwarta ne a bisa sare wa wasu mambobinta albashinsu.

Shugaban kungiyar ta NLC na jihar, Kwamared Hashimu Gital shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke tsokaci dangane da sabon tsarin biyan albashi da aka fitar a jihar, ya bayyana cewar sabon tsarin wanda aka fitar da shi da nufin inganta harkar albashin ma’aikata, ya taba hakkokin ma’aikatan jihar da dama.

Ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga dukkanin ma’aikatan da abun ya shafa da su yi hakuri su gabatar da bukatunsu a rubuce domin kokarin shawo kan matsalar.

Wakilinmu ya shaida mana cewar tuni wasu ma’aikatan suka fara tuturuwar kai kokensu inda aka ce su kai domin dakile wannan matsalar, suna masu fargabar cewar kada kuma matsalar ta zarce har watan gaba, mun jiyo ma’aikata da dama a ma’aikatunsu suna korafi masu zafi wasu ma na danganta matsalar cewar bai kamata a kawo wannan lamarin a watan Ramadan ba, inda suka buga misali da cewar suna tsananin neman kudi hade da tsara yadda za su yi su wajen gudanar da bukukuwan sallah sai kuma ga zaftarewa ta samesu.

A cikin jawabin da gwamnan jihar Bauchi ya yi a wajen bikin ranar demokradiyya wacce ta gudana a dakin taro na rundunar sojin kasa da ke Bauchi, Gwamna Muhammad Abubakar ya sha alwashin cewar babu wani ma’aikacin jihar da ke binsa sisin kwabo na albashi, yana mai cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen biyan ma’aikatan jihar albashinsu a kowani lokaci.


Advertisement
Click to comment

labarai