Connect with us

LABARAI

EFCC Ta Kulle Tsohon Gwamna Ramalan Yero

Published

on


Hukumar yaki da cin hanci da rasahawa da hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFFC) ta kulle tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ramalan Yero a ofishin ta.

Yero an kulle shine tare da tsohon shugaban PDP na jihar Abubakar Gaya Haruna da tsohon sakataren gwamnatin jihar  Hamza Ishak da tsohon ministan muhalli Nuhu Somo Wya.

Mutanen hudu, sun shafe watanni biyu suna suna zuwa ofishin hukumar dake kaduna don amsa tambayoyi.

Wata majiya a hukumar ta bayyana cewar, lokacin da suka je ofishin da safiyar Labar jiya don ci gaba da amsa tambayoyin da ake yi masu, aka kulle su kuma za a gurfanar da su a gaban kotu yau Alhamis.

Majiyar kusa da hukumar wadda bata son a ambaci sunan ta  tace, “gobe za a kai su kotu zan iya tabbatar maka da hakan tsohon gwamnan yana nan tare da mu kuma za a gurfanar dashi a Kotu tare da sauran mutanen uku.”

Yero dai dama yana fuskantar bincike akan rawar da ya taka akan rabon naira miliyan 750 na yakin neman zaben PDP kaffin a gudanar da zaben shekarar 2015.

Anyi kokarin jin ta bakin kakakin hukumar na shiyyar Kaduna Kamaludeen Gebi amma hakan yaci tura har lokacin hada wannan rahoton.

Tsohon gwamnan da sauran an bincike su a satin da ya gabata, inda suka sanya hannu akan wasu takardu da suka shafi binciken da ake yi na zargin badakalar kudin, inda aka umarce su su tafi gida bayan an gama binciken.

Amma an tsare su jiya Laraba saboda gurfanar dasu da za a yi gobe Alhamis.


Advertisement
Click to comment

labarai