Connect with us

MANYAN LABARAI

Dino Ya Bayyana Da Sabon Salo A Majalisa

Published

on


-APC Da PDP Sun Yi Musayar Yawu

-Ya Yi Wa PDP Godiya Ta Musamman

 

A jiya ne Sanata Dino Melaye ya halarci zaman majalisa, inda bayyanar tasa ta haifar da rudani tsakanin Sanatocin jam’iyya mai mulki APC da na jam’iyyar adawa PDP.

Dan majalisar mai wakiltar Kogi ta Kudu ya halarci zaman majalisan ne bayan da ya kwashe fiye da mako uku yana jinya a asibiti.

A jawabinsa a zauren majalisar, Mista Melaye, ya mika godiyarsa ga abokan aikinsa da ‘yan majalisar wakilai da sauran jama’ar Nijeriya a bisa kasancewa tare da shi a lokacin da yake fuskantar matsalar data same shi.

Daga nan Mista Melaye ya kuma mika godiyarsa ga shugabannin jam’iyyaar PDP a bisa taimakon da suka bashi.

Mista Melaye, wanda ya halarci zaman majalisar da bandejin asibiti a wuyarsa, ya kuma bukaci shugaban majalisar Bukola Saraki, daya umurci babban jami’in majalisar ya samar masa kujera a bangaren zaman ‘yan adawa a cikin majalisar, ya kuma sanar da cewa, zai zauna a kusa da tsohon shugaban majalisar, Sanata Dabid Mark, har zuwa lokacin da za a samar masa da wurin zaman, a nan ne wasu Sanatoci suka taimaka masa har zuwa wajen zaman daya zaba.

Ya zuwa yanzu bai baiyana wa majalisar a hukumance cewar ya shiga jam’iyyar PDP ba, yin haka a hukumance na bukatar sai ya rubutawa shugaban majalisar shawarar shiga jam’iyyar adawar, sannan an kuma karanta wasikar a gaban majalisar.

Mutum na farko da ya fara kalubalantar wannan sauya wurin zama na Dino shi ne Shugaban masu rinjaye na Majalisa, Sanata Ahmad Lawan, wanda ya ce, wannan sauya wuri ya sabawa doka ta 56 ta tsarin Majalisar.

Sanata Ahmed Lawan ya ce; “Har yanzu Sanata Dino daya ne daga cikin Sanatocin APC. Ko ba komi ba zauna a bangaren PDP na tsawon shekaru takwas. A nan bangaren APC kuma na zauna na tsawon shekaru uku kenan. Kowanne bangare na san ya kujerun suke. A wannan bangaren na APC muna da kujeru masu armashi da za mu bashi ya zauna, idan har bai wadatu da kujerarsa bane.”

Inda kuma ya umurci mai tsawatarwan Majalisa da ya mayar da Dino bangaren APC.

Sai dai a nashi zantukan, Mataimakin Shugaban Majalisar, Ike Ekweremadu ya ce Melaye na ‘yancin zaban inda zai zauna. Inda ya bukaci sanatocin APC da su martaba ‘yancin ra’ayin Dino din.

Shi ma Shugaban marasa rinjayen Majalisa,  Sanata Godswill Akpabio ya ce, wannan ba wai batun jam’iyya bane. Ya ce, jam’iyyar PDP a shirye take ta amshi duk wani Sanata da ke son dawowa cikinta.

 


Advertisement
Click to comment

labarai