Connect with us

LABARAI

Dangote Ya Ciyar Da ’Yan Gudun Hijira, Ya Bayar Da Gudummawar Naira Biliyan Bakwai A Borno

Published

on


Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar da gudummawar raba kayan abinci da ta saba tana yi a dukkanin watan Ramadan, kamar yadda kuma ta bayar da taimako na musamman ga ‘yan gudun hijira a Jihar Borno wanda ya kai na Naira milyan Bakwai.

Wannan yana zuwa ne dab da shirin da gidauniyar ta Aliko Dangote ke yi a wata mai zuwa na kaddamar da wasu gidaje 200 da ta gina a kan Naira bilyan Biyu.

A hakan, gudummawar abincin da hamshakin dan kasuwan ke rabawa zai ci Naira milyan 150, kamar yadda babbar daraktan gidauniyar ta Aliko Dangote, Zouera Youssoufou, ta shaida mana.

Malama Zouera Youssoufou, da take magana a ranar Litini wajen kaddamar da shirin a Maiduguri, Jihar Borno, ta ce kayan da za a raba wa ‘yan gudun hijirar sun hada da, Shinkafa, Suga, Gishiri, Taliya, Semolina, Garin alkama, Masara da Gero.

Ta ce, su na yin wannan alfarman ne domin agazawa kokarin da gwamnatoocin tarayya da na Jiha ke yi.

Ta ce, ya zuwa yanzun, sun raba gudummawar kayan abincin Naira bilyan 7 ga ‘yan gudun hijirar a Jihar ta Borno.

Malama Zouera Youssoufou, wacce manajan shirye-shirye na Gidauniyar, Musa Bala, ya wakilce ta wajen raba kayan abincin, ta ce, wannan duk yana cikin ayyukan jinkan da gidauniyar ke ci gaba da aiwatarwa a Jihar.

A jawabinsa, Gwamna Kashim Shettima, cewa ya yi, gwamnatin Jihar Boeno da al’ummar Jihar su na farin ciki da Dangote da kuma ayyukan jinkan da yake wa al’ummar Jihar.

Ya ce, Dangote, shi ne mutum kwaya daya tilo da yake bayar da agaji mafi girma ga ‘yan gudun hijirar na Jihar Borno, baya ga gwamnatin tarayya da kuma wasu gwamnatocin Jihohi tun daga lokacin da ‘yan ta’adda suka farmaki yankin na Arewa maso yamma.

Gwamnan ya ce, ayyukan jinkan na Dangote ba su takaitu a ciyarwa da tufatar da ‘yan gudun hijirar kadai ba, wanda ya saba yi tsawon shekaru, jinkan na shi har ya kai ga sake tsugunarwa da ayyukan farfado da su.

Ita ma, shugabar hukumar bayar da tallafin gaggawa na Jihar, Yabawa Kolo, ta bayyana farin cikinta ne da ayyukan jinkan gidauniyar ta Dangote, a madadin bakidayan ‘yan gudun hijirar.

Ta baiwa gwamnan tabbacin hukumar nata za ta yi aiki tare da jami’an gidauniyar wajen ganin wadanda suka cancanta ne kadai za su amfanu da gudmmawar.

Daganan ne sai gwamnan da sauran manyan baki suka zagaya domin duba rukunin gidajen da gidauniyar ta Dangote ta gina wacce Aliko Dangoten zai kaddamar da su a watan gobe.


Advertisement
Click to comment

labarai