Connect with us

LABARAI

’Yan Kunan Bakin Wake Sun Kashe Mutum 3 A Borno

Published

on


‘Yan kunan bakin wake da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar nan ne masu jihadi na Boko Haram sun kashe akalla mutum 3 a Arewa maso Gabashin Nijeriya, kamar yadda ma’aikatan bayar da agajin gaggawa suka sanar ranar Litinin.

‘yan kunan bakin yaken sun tarwatsa bam din da suke dauke dashi ne cikin wani gida da kuma kusa da masallaci a unguwan Mashamari dake Konduga, kilomita 35 kudu maso arewa da Maiduguri babban binin jihar Barno da yammain ranar Lahadi.

“Mutum 3 suka rasa rayukansu a harin da aka kai yayin da mutum 7 suka ji munanan raunuka” inji Bello Danbatta wani jami’in tsaro na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Barno (SEMA) ya bayyana wa kafar watsa labarai na AFP.

“Daya daga cikinsu ta tarwatsa kanta ne a kusa da wani masallaci yayin da mazauna unguwan ke shirin yin sallar magrib, bayan wani dan lokaci sai biyun ya tashi a wani gida” inji Danbatta wanda yana daga cikin wadanda suka zakulo wadanda harin ya shafa.

Amma a nasa ba’asin, Ibrahim Liman, wanda yana daga cikin kungiyar fararen hukan daka taimaka wa jami’an sojoji wajen yakan ‘yan Boko Haram, ya ce, mutum biyu daga cikin wadanda harin ya rutsa dasu sun rasu a kan hanyar zuwa asibiti, haka ya zama ken an mutum 5 suka rigamu gidan gaskiya.

Wannan harin ya faru ne kusan mako biyu da aka kashe yan kungiyar fararen jhula dake taimaka wa sojoji su 5 a lokacin da wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa bam din dake boye a jikinsa a daidai shingen binciken motoci dake bayan garin Konduga.

Yakin da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da yi na tsawon shekara 7 domin samar da kasa mai tafiyar da mulkin  musulunci ya yi sanardiyar rasuwar fiye da mutum 20,000, yayin da yakin ya tarwatsa mutum fiye da Miliyan 2.6 daga gidajensu a Nijeriya. Tuni tashin hankalin ta watsu zuwa kasashe makwabta irinsu Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Amma dai tuni aka raunata karfin kungiyar ‘yan ta’addan a yakin da ake yi a yankin na Afrika, inda aka fi samun sojoji daga Nijeriya, amma duk da haka irin wannan kunan bakin wake na ci gaba.

‘Yan ta’addan sun shi ga amfani ‘yan kunan bakin wake, inda suke amfani da mata da ‘yan mata, inda suke kuma harin shingen binciken sojoji da masallatai da kasuwanni da tashoshin mota da kuma makarantu. Mutun fiye da 86 suka mutu ranar 1 ga watan Mayu 2018 a lokacin da wasu tagwayen bama bamai suka tashi a garin Mubi dake jihar Adamawa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai