Connect with us

LABARAI

Shugaban Cocin Katolika Ga Buhari: Yunwa Ta Addabi ’Yan Nijeriya

Published

on


Babban Shugaban Cocin Katolika a Nijeriya, Nicholas Okoh, ya kirayi gwamnatin Shugaba Buhari da ta hanzarta yin wani abu domin magance yunwan da ta addabi al’umma a kasarnan.

“Akwai fa yunwa ko’ina a cikin kasarnan, ya wajaba gwamnatin tarayya ta hanzarta yin wani abu kafin abin ya kara tabarbarewa,” in ji Okoh, a ranar Lahadi.

Cikin jawabin na shi ga shugaban kasa wanda aka yi a Cocin, Basilica of Grace Gudu, da ke Abuja, Babban Limamin Okoh, cewa ya yi, baya ga yunwan da ta dabaibaye ma’aikatan kasarnan, ya kuma kamata a dubi lamarin ‘yan Fensho su ma.

Ya yaba wa gwamnatin tarayya kan sauraran koken ma’aikata da ta yi na neman karin albashi, inda ya ce, gaskiyan halin da tattalin arzikin kasarnan ke ciki ne ya wajabta sauraran koken na su.

Ya kuma ce, ya wajaba a magance yawaitan rashin aikin yi da shi ma ya addabi kasarnan cikin gaggawa.

Ya kuma yi kira ga duk dan Nijeriyan da ya cancanci jefa kuri’a da ya tabbatar da ya yi rajista kafin zaben 2019. Duk rintsi, ya fi kyau ka daure ka yi rajistan da a ce ka zama dan kallo a lokacin zaben.

Ga masu neman a sake zaben su ya ce, “Na kalubalance ku da ku yi dubi da halin da kasar ke ciki a halin yanzun, kafin ku nu na kanku tukunna.

“Rashin sanin ya kamata ne ga duk wani da yake son al’umma su kara zaben sa, bayan sun zabe shi a baya, a maimakon ya daukaka rayuwarsu sai ya tsaya yana ta zagin gwamnatocin baya. ‘Yan Nijeriya sun gaji da halin ci baya, gaba muke son mu ci.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta yi wani abu cikin hanzari domin magance matsalar kashe-kashen da ya ki ci-ya ki cinyewa a kasarnan.

“Idan ba ku magance hakan ba, ba kuma wanda zai saura domin ya zai zabe ku a shekarar 2019 in duk an kashe kowa.”

Mista Okoh, ya yaba ma gwamnati kan kin yarda da ta yi da amincewa da auran jinsi a kasarnan.


Advertisement
Click to comment

labarai