Connect with us

LABARAI

Neman Ilimi Shi Ne Mafita Ga Musulmi –Shekh Hamza Badikko

Published

on


An shawarci al’ummar musulmi, musamman matasa das u kara tashi tsaye na ganin sun sami ilimin addinin musulunci domin su tsira daga fadawa kungiyoyin dab a na musulunci ba.

Wannan shawarar ta fito ne daga fitaccen malamin nan da ke garin Kaduna, kuma shugaban kungiyar ciyar da addinin musulunci gaba [AL-THAKALYN CULTURAL FOUDATION], Shekh Malam Hamza Muhammad Badikko, jim kadan bayan kammala taron kungiyar na kasa, da taron ya gudana a Zariya.

Shekh Malam Hamza Muhammad Badikko ya ci gaba da cewar, rashin tashi tsaye ga akasarin matasa a yau, ya sa matasan ke fadawa matsalolin shiga kungiyoyin da ba su da alaka da addinin musulunci, sai ka ga suna durkusar da musulunci da kuma musulmi, maimakon ciyar da addini da al’ummar musulmi gaba.

Kamar yadda malamin y ace, dalibin ilimi wajibi ne a gareshi, in ya tashi neman ilimi, ya bi ka’idar da musulunci ya tsara, na gudanar da bincike ga duk inda malami nagari yak e, da kuma inda ya yi karatu, in an yi haka, kamar yadda Shekh Malam Hamza Badikko ya ce, dalibin ilimi zai sami ilimi nagari da zai zama masa alheri, duniya da kuma lahira.

Samun ilimi mai inganci, a cewar Shekh Badikko, zai yi wa dalibin ilimi jagora ya gudanar da binciken duk wani batu na ilimi da ya je gareshi, binciken zai sa dalibin ilimin ya sami ilimiai inganci, da zai katange shi daga tsunduma matsalolin da musulunci bai yadda da su ba.

Da kuma malamin ke tsokaci kan taron shekara da suka kammala ya ce,sun shirya taron ne, domin tunatar da mahalarta taron muhimmancin neman ilimi da kuma muhimmancin da ke tattatre da Imam Mahadi, da ya shafi tarihinsa da kuma shin zai dawo  domin ciyar da musulunci gaba ko kuma a’a.

A dai ganawar da wakilinmu ya ya yi da Shekh Hamza Muhammad Badikko, ya tunatar da malamai na nauyin da ke kan su, kan lamurran da suka shafi siyasa, kamar yadda y ace, a yau, malamai su shiga tsakiyar siyasa, matsala ce babba da ya dace  a lura shi.

Ya kara da cewar, ya dace malamai su tsaya su gyara halayyar mutane kan yadda ake siyasa a Nijeriya a yau, da kuma yadda ake yin zabe, ba zabe ake yi ba, sayen kuri’u ake yi,ba zabe ba, a cewar Shehin malamin.

Shekh Badikko,ya tabbatar da cewar, in har aka sami nasarar baragurbin malamai sun dai na furta abin da ‘yan siyasa da kuma shugabanni ke bukata, ko kuma suke so, sun rungumi shirin gyara kasa da kuma al’ummar kasa, za a wayi gari, malamai sun rungumi siyasa da hannu biyu, in ma an sami dama su shiga takara ko wace kujera ta wakilci ko kuma ta shugabanci a fallen gwamnati uku.

A karshen ganawarsa da wakilinmu, Shekh Malam Hamza Muhammad Badikko, ya shawarci al’ummar musulmi da su tsayu ga tsarin musulunci a duk inda suka tsinci kansu, rashin yin haka ga al’ummar musulmi, kamar yadda malam y ace, shi ya sa ake samun matsaloli ma su yawan gaske, da ake wa addinin musulunci ne,wanda abubuwan ba su yi kama da addinin musulunci ba, inji shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai