Connect with us

LABARAI

Matar Kakakin Majalisar Tarayya Ta Tallafa Wa Mata Manoma 7,000 A Bauchi

Published

on


A makon jiya ne uwar gidan Kakakin Majalisar Tarayya Misis Gimbiya Yakubu Dogara ta kaddamar da rabon kayyakin noma na zamani wa mata da matasa su dubu bakwai domin karfafansu kan hidimar noma da kuma inganta tattalin arzikin jama’an jihar.

Wannan shirin na matar Dogara, na daga cikin shirinta na tallafa wa marasa galihu ne, wacce ke zuwa a karkashin shirinta mai suna ‘Sun Of Hope Foundation’, wadanda suka ci gajiyar shirin sun fito ne daga mazabar Dass, Bogoro da kuma Tafawa Balewa.

Ababen da ta raba wa namoman sun hada da irin masara, taki, shinkafa, da kuma maganin kashe ciyayi da kwari na zamani masu inganta gona.

A lokacin da take jawabinta, uwar gidan Dogara, wacce ta samu wakilicin Ko’odinetan gidauniyarta na ‘SUN of Hope’ Mrs Darambi Kefas ta bayyana cewar wannan tallafin nata zai iya kawo karshen matsatsin talauci da mata ke fama da su a gidajen aurensu.

Uwar Kakakin Majalisar Gimbiya Dogara ta bayyana cewar a shirye take ta ci gaba da samar da hanyoyin da suka dace domin taimaka wa ‘yan uwanta mata ta hanyoyin dogora da kai a maimakon jiran na mazajensu.

Ta bayyana cewar iyaye mata suna da rawar da za su taka wajen taimaka wa kawukansu da ‘ya’yansu ta kuma bayyana cewar zaman kashe wando da zaman jiran sai mai gida ya kawo yanzu ba na matan wannan zamanin ba ne “Lokacin da mu mata za mu tsaya sai mazajenmu sun kawo mana ya wuce, domin mu mata muna da muhimmaci muna kuma da damarmakinmu a hanunmu da ya dace mu bi domin taimaka wa kawukanmu da kuma ‘ya’yanmu,” In ji Gimbiya Dogara.

Ta bayyana cewar a shekarar da ta gabata ma ta raba wa mata su 3,500 irin shinkafa domin bunkasa musu tattalin arzikinsu, “Wannan shimkafar da bayar, na tabbatar nan da wata hudu kowace mace za ta kasance tana da akalla buhu 10 ko sha biyu. domin a kowace kiloggiram daya za a samu buhu daya, kun ga nan da wata hudu kowace mace daga cikinku za ta mallaki buhun shinkafa hudu. Idan muka jure muka ci gaba da fafatawa nan gaba kadan kowace mace za ta dogara da kanta a maimakon jiran mai gida ya kawo, zamu zama masu arzikin taimakon kanmu da wasu”. In ji Dogara Gimbiya.

Matar Dogarar wacce ta kafa gidauniyar nan mai suna ‘SUN of Hope Foundation’ ta bayyana cewar wannan kungiyar an kafa tane domin taimaka wa yara kanana da kuma iyayensu mata domin rage musu kuncin rayuwa da kuma dawainiya.

Da yake karin haske, Babban mai tallafa wa Kakakin Majalisar Tarayya kan hulda da ‘yan jarida, Iliya Habila ya bayyana cewar mata dubu 7,000 ne suka ci wannan gajiyar a wannan shekarar ta 2018, “Mata da matasa dubu bakwai ne suke cin gajiyar wannan shirin na uwar gidan Kakakin Majalisar Tarayya. A cikin wannan dadin, mata dubu 3,500 sun samu tallafin ingattaccen irin shinkafa da takin zamani hade da maganin ciyawa,”

“Matasa kuma su dubu uku da dari biya 3,500 aka basu irin masara, taki da kuma maganin ciyawa,” In ji Iliya.

Ya bayyana cewar wannan tallafin dukkanin wani mazaunin kauye kuma mai filin noma a garunsu matukar ya samu irin wannan tallafin kowani manomi ko manomiya ta samu aza tubalin yin arziki, yana mai cewa noma tushen arziki ne domin haka da bukatar wadanda suka ci gajiyar shirin su maida hankulansu domin yin nomad a wadannan kayyakin noma na zamani da suka samu.

Iliya Habila ya bayyana cewar a shekarar da ta gabata a sakamakon rabon kayyakin noma da Matar Dogara ta yi, an samu mata manoma da dama da suka samu zarafin habaka tattalin arzikinsu wanda ya ce kawo yanzu an samu sakamako mai kyau kan hakan.

Da take jawabin godiya a madadin wadanda suka ci gajiyar shirin, Esther Bitrus ta bayyana cewar wannan tallafin nomad a suka samu daga matar Dogara za su yi amfani da shi wajen habaka sha’anin nomarsu, tana mai bayanin cewar sun samu zarafin da za su bi domin kyautata noma domin yakar talauci a tsakaninsu.

Ita ma Seray Nuhu ta ce “Za mu yi amfani da wadannan kayakkin domin inganta noma. Za kuma mu sanya a gonakanmu domin ganin mun samu sakamako mai kyau,”

 


Advertisement
Click to comment

labarai