Connect with us

LABARAI

Garkuwan Talba Ya Zama Cikasoron Minna

Published

on


Mai martaba sarkin minna, Alhaji Umar Faruk Bahago ya nemi masu rike da sarautan gargajiya a masarautar da su zama jakadu na kwarai wajen anfani da hikimarsu dan samar da zaman lafiya a cikin al’umma. Sarkin ya yi jan hankali ne a lokacin da tawagar Garkuwan Talba kuma Cikasoron Minna na farko, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida suke je yi mai godiyar sarautar a fadarsa.

Sarkin ya ci gaba da cewar manufar bada sarautu ga nagartattun mutane ita ce fadada masarauta da samar wakilci na gari, masarauta na farin cikin fadada ta hanyar bada sarautu dan samar da wakilcin da za taimaka wajen sanya ido a cikin al’umma. A koda yaushe ana son mai rike da sarauta ya zama uba mai taimakawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Sarautar Cikasoron a masarautun kasar Hausa guda hudu ne kuma duk ‘Yayan da ke da nasaba da sarauta ce aka baiwa, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida shi cikon na biyar da masarautar minna ta nada ma wannan sarautar.

Da yake jawabi ga al’ummar masarautar, sabon Cikasoron, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida, yace wannan sarautar masarautar minna ta karrama ‘yayanta ne masu da’a da biyayya, dan hakan zan yi anfani da wannan damar dan godiya ga urban mu mai martaba sarki akan amince min da yayi bisa bani sarautar Cikasoro, aikin jama’a dama dan ba muka sanya, da yardar Allah da shawarwarin al’umma zamu tsaya dan ganin mun yiwa masarauta aiki yadda ya kamata.

Lallai Cikasoro babban al’amari ne muna kara godiya ga mai martaba da wadanda suka amince dan mu hada hannu mu yi aiki tare, mu jaddadawa masarauta duk abinda aka ga ya kamata a umurce kai tsaye, domin ci gaban masarautar minna ita ce burin mu. Babban aikin mu shi ne hada kan jama’a, wayar da kan jama’a muhimmancin hada da zaman lafiya, domin ita zaman lafiya ita ce gaba da komai kuma ita ke samar da ci gaban kasa da bunkasar tattalin arziki.

Cikasoron ya karyata zargin kabilanci da ake zargin masarautar da shi, inda yace tun kan rasuwar mahaifin mai martaba Hausawa ke rike da sarauta a masarautar nan, kuma ko bayan zuwan shi akwai Hausawa da dama irin su Talban Minna, Sardaunan minna da daman su bagwarawa ba ne kuma masarauta na ci gaba, dan haka masu ra’ayin batanci da kirkirar karya su daina, mai martaba, Dakta Umar Faruk Bahago, uba ne na kowa.

Alhaji Aliyu Umar, sarkin shanun gundumar makera kuwa yabawa masarautar yayi akan yadda ta ke kokarin hada kan al’umma mabambantan kabilu. Ya ci gaba da cewar wannan nauyi da mai martaba ya dora mana ya bamu amanar kulawa da jama’a ne, ya zama wajibi mu hada kai wajen kawo ci gaba a masarautar, kasar nan na bukatar hadin kai, tana bukatar aiki tare wajen kau da kabilanci, don zamu aiki wurjanjan wajen mun dawo da hankulan matasa a irin yanayin da suka tsinci kawunansu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai