Connect with us

LABARAI

Atiku Ya Nada Tsohon Gwamna A Matsayin Sarkin Yakin Takararsa

Published

on


Nan ba da jimawa ba, tsohon Mataimakin Shugaban kasarnan, Atiku Abubakar, zai shelanta nadin da ya yi wa, tsohon gwamnan Jihar Ogun, Gbenga Daniel, a matsayin sarkin yakin kamfen din zabensa a matsayin Shugaban kasarnan, a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP.

A babban taron Jam’iyyar ta PDP da ya gabata, Gbenga Daniel, ya yi takarar neman shugabancin Jam’iyyar ta PDP.

Cikin wata sanarwa da majiyarmu ta samu wacce shi da kansa Atikun ne ya sanya wa hannu, inda ya bayyana wa tawagar kamfen din na shi nadin da ya yi wa Gbenga Daniel, inda yake maraba da zuwansa, ya kuma bayyana shi da cewa, Gbenga, babban fata ne ga kamfen din neman zaben na shi.

“Ina farin cikin sanar da ku nadin da na yi wa, Mai Girma, Otunba Gbenga Daniel, (wanda aka fi kiransa da, “OGD”), a matsayin babban daraktan kamfen din kungiyar, ‘Atiku Campaign Organisation,” kamar yadda wani sashen na sanarwar ya nu na.

“OGD, tsohon gwamna ne a Jihar Ogun har karo biyu, sannan kuma kwararren Injiniya, hamshakin dan kasuwa kuma dakakken dan siyasa ne. Cikakken masanin siyasar Nijeriya ne, yana kuma da abokanai da masoya ko’ina a Nijeriya, wannan kadan ne daga cikin hajar da zai zo mana da ita a cikin wannan tafiyar na mu.

“Ba na shakkan, OGD, zai albarkaci wannan tafiyar namu, kan haka nake kwadayin yin aiki tare da shi, domin ya jagorance mu zuwa ga nasara a watan Fabrairu 2019.

“A matsayin, OGD, na babban daraktan kamfen dinmu, duk wani abu na wannan tafiyar ya rataya a wuyansa ne. Wannan ya hada da neman jama’a da shirya taruka, sanarwa da sadarwa, sha’anin kudade da yadda ake kashe su. Ina shirin kafa wani kwamitin neman gudummawan kudi na daban, wanda za su yi aiki tare da shi domin tsara yanda za a kashe kudi a wajen kamfen.

“Dukkanin ma’aikatan tafiyar namu, su na karkashin babban daraktan namu ne, shi ke kuma da alhakin daukan ma’aikata da duk wani abin da ya shafi kamfen din namu, duk na mallaka ma shi iko a kansu.

“Daga yanzun, ni aiki na ya takaitu ne da ci gaba da tuntuban masu ruwa da tsaki, a Jam’iyyar namu ta PDP, da ma sauran Jam’iyyu bakidaya. Duk lamarin kamfen ko abin da ya shafi ma’aikatanmu, sai a mika su ga babban daraktan kamfen din namu cikin hanzari.

“Kaitsaye ne Babban daraktan namu zai rika tuntuba ta.”

Majiyar namu ta jiyo mana daga wata majiya ta cikin gida cewa, Atiku, zai shigo siyasar gadan-gadan da zarar ya kaddamar da Gbenga Daniel ga al’umma.


Advertisement
Click to comment

labarai