Connect with us

LABARAI

2019: Duk Wani Mai Sha’awar Takara Ya Aijye Aikinsa Kafin 29 Ga Watan Mayu –Gwamna Ortom

Published

on


Gwamna Ortom na jihar Benue ya umurci ma’aikatan Gwamnatin jihar masu sha’awar tsayawa  takara a 2019 su ajiye aikinsu kafin lokaci yayi.

Gwamna Samuel Ortom ya ce, duk wanda bai ajiye aikinsa ba kafin 29 ga watan Mayu zai iya fuskantar hukuncin wasu lauyoyi sun ce umurnin gwamnan ya yi daidai da dokar aikin gwamnati da ta yi hani ga ma’aikatan su shiga takara ba tare da ajiye aikinsu ba

A halin yanzu da ake ta shirye-shiryen tunkarar babban zaben kasa na shekarar 2019, Gwaman Samuel Ortom na jihar Benue ya umurci dukkan masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da ke sha’awar takara a zaben su ajiye ayyukansu.

Gwamna Ortom ya sallami ma’aikata da ke niyyar shiga siyasa a wata sanarwa da ta fito daga bakin babban sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Anthony Ijohor (SAN). Gwamnan ya umurci masu niyyar takarar su ajiye ayyukansu kafin ranar 29 ga watan Mayu ko kuma su fuskanci hukunci.

Gwamnan ya yi gargadi a kan fara yakin neman zabe kafin ajiye aiki, inda ya ce aikata hakan laifi ne da dauke da hukunci saboda saba umurnin gwamnan.

Wasu lauyoyi da suka nemi a sakayya sunayensu sun shaidawa kamfanin dillancin labaran kasa (NAN) cewa gwamnan yana da ikon gindayawa ma’aikatan ajiye ayyukansu tunda dama nada su aka yi.

Sun kuma yi karin bayani da cewa dama dokar aikin gwamnati ta hana ma’aikata tsunduma hannunsu cikin takarar siyasa a yayin da suke rike da wata mukami ko aikin gwamnati.


Advertisement
Click to comment

labarai