Connect with us

LABARAI

Za Mu Kawo Karshen Kisan Mummuken Binuwai –Saraki

Published

on


Shugaban Majalisar Dattawan Tarayya, Bukola Saraki ya ba al’ummar Binuwai tabbacin cewa za a kawo karshen yawaitar kisan mummuken da ake fama da shi a fadin jihar.

Haka kuma ya bayyana cewa, Majalisar Dattawa za ta yi iyaka kokarinta wurin tabbatar da an yi adalci ga kauyawan da mahara suka salwantar da rayukansu a fadin jihar.

Saraki ya yi wannan jawabin ne a jiya yayin wata ziyara da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira dake Abagana dake makwabtaka da garin Makurdi, domin ya taya yaran dake sansanin murnar zagayowar ranar yara ta duniya.

“Ina son tabbatar muku da cewa, a matsayina na Shugaban Majalisar Dattawa, da ni da abokan aikina ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai ranar da muka tabbatar da an samar da tsaro ga al’ummar Jihar Binuwai. Sannan kuma za mu tabbatar da cewa an yi muku adalci.” inji shi

Shugaban Majalisar Dattawan ya kara da cewa, akwai fata nagari ga kananan yaran Nijeriya, musamman ma wadanda suke mabambantan sansanin ‘yan gudun hijira a fadin tarayyar Nijeriya, ciki har da wadanda ke Binuwai. Ya ce, dole ne a matsayinsu na shugabanni su tabbatar da inganta rayuwar wadannan yara don gobensu ta yi kyau.


Advertisement
Click to comment

labarai