Connect with us

LABARAI

Yaki Da Rashawa: ‘Transparency International’ Na Yi Wa Nijeriya Zagon Kasa –Minista

Published

on


Gamnatin tatayyar Nijeriya ta gargadi hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ta duniya (Transparency International) da sauran kugiyoyi fararen hula na cikin gida masu alaka da ita, dasu gaggauta daina yin zagon kasa ga yakin da gwamnatin Nijeriya ke yi da cin hanci da rashawa.

Ministan watsa labarai da al’adu, Lai Mohammed, ne ya yi wannan gargadin a lokacin yake maraba da tawagar hukumar TI karkashin jagorancin shugabar hukumar Misis Delia Rubio, a Abuja ranar Jumma’a data gabata.

Jami’in watsa labaran Ministan, Mista Segun Adeyemi, ya sanarwa da manema labarai a Abuja ranar Asabar, inda ya ce,

Ministan ya bukaci kungiyar kasa da kasa masu yaki da cin hanci dasu tallafa wa kokarin da shugaba Muhammadu Buhari keyi maimaikon kushe kokarin da suke yi.

Ya ce, kungiyar TI da sauran ire irenta na cikin gida basu bayar da taimakon daya kamata ba maimakon haka ma sai yin tir da kokarin gwamnati suke yi.

Minstan ya ce, kungiyar ta ce, an yi son rai a lokacin da gwamnatin ta ce, mutane 55 sun sace Naira Tiriliyan 1.34 a tsakanin shekarar 2006 zuwa shekarar 2013

Ya kuma ce, a lokacin da gwamnati ta wallafa sunayen barayin gwamnati, bayan da yan adawa suka kalubalancemu, wasu bangaren kungiyoyin fararen hula suka koma suna kokarin aiki da bangaren barayin.

Mista Mohammed ya ce, Nijeriya na samun nasara ne yaki da cin hanci da rashawa saboda shugaban kasa da duk duniya suka amince da halayensa ne ke jagoranta yakin.

“Wannan gwamnatin ra dukufa fiye sauran gwamnatin da aka taba yi wajen yaki da cin hanci da rashawa.

“Nijeriya bata taba samun gwamnati mai adalci kamar ta shugaba Buhari ba.

“Hatta yan adawa sun tabbatar da baya karfafa harkar cin hanci da rashawa. Inji shi.

Mista Mohammed ya kuma lura da cewa, wannan gwamnatin ba wai tana yaki da cin hanci kawai bane tare da hukunta wadanda aka kama, tana kuma ilimantar da jama’a a kan tafiyar da harkar gwamnati ba tare cin hanci da rashawa ba.

Ya kuma kawo misali da shirin nan na ‘Change Begins With Me’ shirin da gwamnati kirkiro domin canza tunanin yan kasa.

Ministan ya kuma yi bayanin cewa, Nijeriya na gudanar da milkin tsarin tarayya ne, a wannan tsarin gwamnati tatayya bata da iko a kan harkokin dake tafiya a jihohi.

Ya kuma yi korafin cewa, barayin gwamnati na amfani da kudaden da suka sata wajen yada labaran karya a kan wannan gwamnati, saboda sun tabbatar da in shugaba Buhari ya sake cin zabe zasu shiga matsala.

Daga nan Ministan ya bukaci kungiyar TI da sauran mukarrabanta na cikin gida dasu yi kokarin fahintar matsalolin dake gaban kasar nan a kokarinta na yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.

Ya kuma bukaci karin taimako daga TI wajen wayar da kai da horar da jami’an gwammnati.

A nata jawabin, shugabar kugiyar TI ta ce, ta zo Nijeriya ne a ziyarar ta farko a Afrika saboda Nijeriya na iya jagorantar Afrika gaba daya a yaki da cin hanci da rashawa.

Ta ce, dokar aikin TI ya bata karfin bayar da tallafi ta hannun kungiyoyi masu zaman kansu somin yaki da cin hanci da rashawa.

Ta kuma ce, a lokacin da gwamnati ke kokarin yaki da cin hanci da ya kamata a samar da yanayin yin aikin gwamnati a bayyane ba tare da boye boye ba.

“Bamu a cikin kungiyar adawa a ko ina a duniya.

“Mu kungiya ce mai zaman kanta, muna kuma aiki a kasashe fiye da 100, mu ba abokan gaba bane, mun zo bayar da namu taimakon me” inji ta.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai