Connect with us

LABARAI

Ranar Yara: Buhari Ya Shawarci Jami’an Tsaro Da Sauran Al’umma

Published

on


Shugaba Buhari, ya kalubalanci sassan tsaro na kasarnan, Iyaye, Sarakuna da Malaman Addini da su tashi tsaye su dauki tsauraran matakai domin magance yawaitan cin zarafin yara kanana da ake yi.

Shugaban ya yi wannan kiran ne cikin sakon kaddamar da ranar yara ta kasa da aka yi a Abuja ranar Asabar.

Ya yi nu ni da taken bukin na bana, “Samar da zaman lafiya ga yara kanana; Hakki ne da ya hau kan kowa,” inda ya ce hakan wata dama ce ta samar da zaman lafiya da kuma cikakken tsaro ga yaran kanana.

Ya ce, duk masu ruwa da tsaki kan lamurran yaran da suka hada da, kungiyoyi, masu rajin kare hakkin dan Adam, da ma al’umma bakidaya, ya wajaba da su tabbatar da tsaron lafiyar yaran a gidajensu, makarantu, kasuwanni, wuraren ibada, kan tituna da koma ina ne kuma a kowane lokaci.

A cewar shi, bikin na wannan shekaran, ya ba shi daman kara tabbatar da aniyar gwamnatinsa ta kare yaran.

“Wannan rana ce ta sake yin dubi kan irin hobbasan da muka yi a matsayinmu na shugabanni, Iyaye wajen kare lafiyar yaran namu. “Idan za ku iya tunawa, daya daga cikin manufofin wannan gwamnatin shi ne, samar da ingantaccen ilimi ga yaranmu a matsayin wani ginshikin tattalin arzikinmu da kuma ci gaban kasarmu.

Ya ce, “Ina matukar jin dadin irin rawar da yaran namu ke takawa, da kuma irin hasken da ke fuskantar su a nan gaba.

“Wannan ne daya daga cikin dalilan da ya sanya muka mayar da hankali wajen ciyar da yaran a makarantun su, domin samar da nagartattun yara masu koshin lafiya.

Ya ce, a lissafi na baya-bayan nan, sama da yara milyan 8.2 ne a Jihohi 24 muka ba su abinci a makarantun su kullum kyauta, ya kara da cewa, muna hakan ne a makarantu, 45,000 na kasar nan.

Ya kuma yi kira ga iyaye da ka da su gajiya wajen tura ‘ya’yansu musamman ‘ya’ya mata zuwa makarantu, domin karatunsu ya na rage yawaitan matsaloli wajen haihuwa da kuma hana yin auren wuri.

Ya na kuma kara yakan jahilci da kuma rage talauci. Akwai karin maganan da ke cewa, ‘Karantar da mace, tamkar karantar da al’umma ne.”

Ya yi nu ni da cewa, tun zuwan wannan gwamnatin, ta mayar da hankalinta ne wajen magance matsalolin yara. Ya ankarar da cewa, a shekarar 2015, gwamnatinsa ta kaddamar da shirin yaki da tursasawa yara, wanda aka yi bikin sa a shekarar 2016.

“A watan Nuwamba 2016, mun kaddamar da shirin yaki da yi wa yara kanana aure, domin mu tabbatar da yara da yawa sun ci moriyar kuruciyarsu, mu kuma kare su daga dukkanin hadurra.

Ya ce, “Wannan gwamnatin ta yi namijin kokari ainun wajen kare hakkokin yaran Nijeriya, a sakamakon hakan ma aka bayyana Nijeriya a matsayin wata kasa abar koyi wajen yaki da tursasawa yara kanana.

“Na kuma tabbata wannan nasarar namu ne bakidaya, ina kuma bukatarmu da mu ci gaba da hakan.

Ya ce, a wani yanki na kokarin da muke yi na tabbatar da tsaron lafiyar yaran da kuma safarar su, gwamnati ta umurci dukkanin makarantun ta, ta kuma shawarci dukkanin sauran makarantu da su tabbatar da sun samar da cikakken tsaro ga dailiban na su a makarantun.

Shugaba Buhari, sai ya nu na jin dadinsa ga dukkanin sassan jami’an tsaro na kasarnan a kokarin da suke yi kawo yanzun. Ya kuma umurce su da su ninka wannan kokarin na su wajen kare lafiyar yaran daga kowane irin hadari, kamar yadda tsarin mulkin 1999 ya ba su kan hakkin yara.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai