Connect with us

LABARAI

Ma’aikatan Lafiya Na Bogi 6,000 A Ka Bankado A Sakkwato

Published

on


Bayan kammala shirin tantancewa kan ma’aikatan lafiya 13,000 na Jihar Sakkwato, an gano cewa, guda 6000 duk fatalwowi ne, Gwamna Aminu Tmbuwal, ne ya shaida hakan.

Ya fadi hakan ne wajen kaddamar da karamar cibiyar lafiya ta Gagi, da kuma dakin haihuwa.

Tambuwal, ya kuma bayyana aniyar gwamnatinsa na sake daukan wasu ma’aikatan lafiyar 400, domin bunkasa sashen na kula da lafiya a Jihar.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin na shi na bunkasa sashen masu ciki da kuma allurorin rigakafi.

A cewar shi, binciken baya-bayan nan, ya nu na cewa,gwamnatin na shi ta sami ci gaba da kashi 43 na allurorin na rigakafi.

A na shi jawabin, Kwamishinan lafiya na Jihar, Dakta Balarabe Kakale, cewa ya yi, shawarar ta samar da dakin haihuwan ta taso ne bisa la’akari da cewa, mafiya yawan matan karkara a Jihar ba sa zuwa Asibitoci domin haihuwa.


Advertisement
Click to comment

labarai