Connect with us

LABARAI

Duk Dan APC Da Jam’iyyar Ta Zalunce Shi Ya Zo Mu Yi Masa Adalci -Jam’iyyar PDP

Published

on


Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi shela wa dukkanin wani dan APC kama daga shugaba ko kuma wani mambo hade da gungu APC ko wanda ke neman wani shugabancin jam’iyyar a matakin Gundumawa, Karamar hukuma da kuma jiha wadanda jam’iyyar ta yi yi musu rashin adalci a zaben maye gurbin jagororin APC da cewar su hanzarta zuwa jam’iyyar PDP tana yin lale marhaban da zuwansu domin yi musu adalcin da suka rasa daga tasu jam’iyyar.

Kakakin Jam’iyyar PDP na jihar Bauchi Alhaji Yayanuwa Zainabari ya yi wannan furucin a hirarsa da ‘yan jarida a Bauchi, yana mai cewa dukkanin wasu gungun ‘yan APC da aka yi musu rashin adalci a shirye suke karbesu su kuma yi musu adalcin da aka gagara yi musu a APC.

Kakakin na jam’iyyar ta PDP a jihar Bauchi, ya misalta zaben maye gurbin jagororin APC a matsayin wani lamari da ke cike da zalumci muraran domin ya bayyana cewar ba zabe suka yi ba, sun kulle kansu a daki ne suka zana wadanda suke so amma ba salin wadanda suka yi wa jam’iyyar wahala ba.

Ya ke bayani kamar haka, “Abun da jam’iyyar APC ta yi a kan zaben shugabanin jam’iyya ba za a kirasa da suna matsala ba, sai dai a ce masa uwar matsala. Saboda kawai wasu tsirarun mutane sun shiga daki suka rubuta abun da suka ga dama, in ka duba ma duk wadanda suka yi wa jam’iyyar wahala, wadanda suka yi gwagwarmaya sosai wa jam’iyyar APC an kawar da su gefe, kila ko don suna kokarin kwatanta gaskiya ko kuma suna fadan cewar gwamnatinsu ta kasa-kasau a dalilinsu na alkawurorin da APC ta zo da su babu daya da ta cimma,”

“A bisa haka ne, wasu suka rike jam’iyyar suka shiga daki suka rubuta abun da suka ga dama. Wannan ba adalci sam a ciki,” In ji PDP.

Ya ce a bisa haka ne suka bude kofa ga dukkanin dan APC da su zo su dawo cikin dangi ma’ana su dawo PDP “Don haka muna kiransu, kodayake daman ‘ya’yanmu ne, su dawo gidansu kawai. Domin yanzu talakan Nijeriya ya yarda cewar jam’iyyar PDP ita ce ta san hanyoyin taimakon talaka radadin da ke damunsa ya yi sauki.

“Amma ita gwamnatin APC babu abun da ta zo da shi illa cewar kullum talaka na cikin ukuba na cikin bala’i, amma sun ki su kawo mafita wa jama’an kasa,” A cewar shi.

Zainabari ya bayyana cewar a yau idan suka sake samun zarafi a zaben 2019 Kakar jama’an Bauchi ta yanke saka domin kuwa sun sauya salonsu daga na da zuwa sabon salo “Jama’an Nijeriya da na Bauchi su kwanda sanin cewar jam’iyyar PDP ta yau ba irin ta jiya bace. Dukkanin kurakuran da suka kaimu ga fadi a zaben 2015 kashi 85 mun gyara su, kuma yanzu ne PDP take da shirye-shirye wajen baiwa dan Nijeriya tsaro, abinci mai nagarta a sau uku na kowace rana, farfado da tattalin arziki da kuma samar da ilimi cikin sauki domin baiwa ‘ya’yanmu ilimi,

Ya kara da cewa, “Ina mai tabbatar maka yau, da APC za ta maida Nijeriya yadda ta zo ta sameta da talakan Nijeriya ya yi murna har azumi sai talakan Nijeriya ya yi domin gode wa Allah a bisa haka, APC ta ruguza komai a kasa nan, Mune kawai masu gyarawa”. Kamar yadda Zainabari ya bayyana.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai