Connect with us

LABARAI

Ba Zan Taba Zagin Buhari Ba, Inji Gwamna Umahi

Published

on


Gwamna Dabid Umahi na Jihar Ebonyi, ya sha alwashin ba zai taba zagin Shugaba Buhari ba, domin wai ya tabbatar da cewa shi dan PDP ne.

Umahi, ya bayyana hakan ne ranar Asabar da dare a Abakaliki, lokacin da yake ganawa da manema labarai wajen liyafar cin abincin dare da ya shirya wa manema labaran a matsayin wani sashe na bikin ranar Dimokuradiyya ta shekarar 2018.

Gwamnan ya ce, wannan matsayin na shi al’adan shi ne, ya kuma karfafa cewa, har gobe Buhari  Shugaban shi ne.

“Duk wadannan maganganun na bar wa Jam’iyyu su, ba domin cewa Buhari yana yin komai a daidai ba, sai don cewa, shi ba Allah ne ba.

“Kila ba zai yiwu ya yi komai a daidai ba, amma ba aiki na ne ba na zagi shugaba na, ni aiki na kawai na sanya a gaba.

“Ba kuma aiki na ne na yi ta kai koken gwamnatocin Jiharmu da suka gabata ba, ni fa aiki na kawai na sanya a gaba a matsayi na na mutumin kirki wanda aka kiraye shi kuma ya amsa.

Gwamnan ya yi nu ni da cewa,cin hanci da karban rashawa ba maganan Jam’iyya ne ba, abin ya shafi daidaikun mutane ne da suka sanya kansu a kan hakan.

“Abin ba a PDP ne yake ba, amma idan wadanda suka fice daga PDP din yanzun suka koma Jam’iyyar da ke mulki ta APC suka kira ‘yan PDP da cewa lalatattu ne, hakan yana nufin su ma sun harbi Jam’iyyar da suka koma cikin ta din kenan.

Ya bayyana cewa, yawan ambatan abokanin adawarsa a Jihar da yake yi a wuraren tarukan karrama shi da ake yi a Jihar, hakan ba ya na nufin yana damuwa da ayyukan su ne ba.

“Ba wani abokin adawar da zai iya yin takarar zabe da ni, saboda ba su kafa komai ba a Jihar face yaudarar mutane.

“Ba kuma Shugaban kasan suke yi wa aiki ba kamar yadda suke karyan hakan, bata kimar Jam’iyyan na su ma kawai suke yi, saboda yawancin su ma ko gida ba su da shi a cikin Jihar nan.

“Su na ikirarin za su yi amfani da karfin sama su murguda zaben 2019 a Jihar nan, amma ai samarin Jiharmu sun gargadi duk mai nufin aikata hakan da ya tabbatar ya rubuta abubuwa biyu, sakamakonsa na bogi da kuma wasiyyarsa,” in ji Gwamnan.

Gwamnan ya zayyana ayyukan ci gaban da gwamnatin na shi ta aiwatar kan fannonin Ilimi, Lafiya, Samar da ayyukan yi, manyan ayyuka da tsaro da sauransu, inda ya yi nu ni da cewa, Jihar Ebonyi sai ta zama Dubai din Nijeriya cikin shekaru takwas da zai yi na mulkin sa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, (NAN), ya hakaito cewa, manema labarai da kuma al’umman Jihar ne a daidaikun su suka yi ta tambayar gwamnan kan abin da ya shafi Jihar da ma kasa bakidaya.

Manyan Jami’an gwamnati, da suka hada har da, Sakataren gwamnatin Jihar, Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnati, ‘Yan Majalisu da wasu wakilan majalisar zartarwar Jihar da sauran su, duk an kulle masu kofar shiga taron kasantuwar sun zo a latti.

Sai a lokacin tambayoyi ne bayan gwamnan ya kammala jawabinsa aka bude masu kofa suka shiga dakin taron

 


Advertisement
Click to comment

labarai