Connect with us

LABARAI

2019: Al’ummar Fagge Na Goyan Bayan Nafi’u Shehu

Published

on


Al’ummar Karamar Hukumar Fagge na ci gaba da nuna goyon bayansu bisa kiran da ake yi wa Alhaji Nafiu Shehu Fagge don fitowa neman takarar majalisar wakilai ta tarayya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP bisa la’akari da irin gudummuwar da yake bayarwa ga ci gaban yankin.

Sun yi nuni da cewa idan Nafiu Shehu ya sami kaiwa ga nasara suna da kyakkyawan zato a kansa kuma zai taimaka sosai wajen kawo ci gaban yankin bisa la’akari da yadda a yanzu ma yake kokarin tallafa wa al’ummar yankin ta fannoni daban-daban don kyautata rayuwarsu.

Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar Fagge sun bayyana cewa za su baiwa wannan takara goyon bayan da ya kamata don kai jam’iyyar PDP ga nasara, ta ganin an tsaida wadanda suka dace da bukatun jama’a.

Saboda haka suka bayyana cewa ga dukkan alamu suna jin irin kyakkyawar shaida da yawancin al’ummar Fagge ke bayarwa akan Alhaji Nafiu Shehu da ake ganin zai karbu a cikin jama’a.

Sun yi nuni da cewa, ba su da wani zabi sai na abin da suka ga al’umma suke da bukata, kuma suna nuna yabawa da kulawa da abin da Alhaji Nafiu Shehu yake yi, don haka su bukatarsu kaiwa ga nasara.

Al’ummar Faggen suna da bukatar mutum mai jajircewa da kaifin basira da kyakkyawan tunanin son kawo ci gaba ga yankin, kuma ga irin shaida da mutane suke bayarwa akan irin kulawa da yake ga jama’ar Fagge, ya kamata a mara masa baya don kaiwa ga nasara.

Alhaji Nafiu Shehu yana ci gaba da samun yabon jama’a bisa irin kokarin da yake bayarwa wajen taimaka wa ci gaban jama’a, musamman ma a cikin wannan wata na azumi.


Advertisement
Click to comment

labarai