Connect with us

LABARAI

Kallo Ya Koma Sama Bayan Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

Published

on


A Larabar nan ne aka samu wata wasikar da mataimakin gwamnan jihar Bauchi Injiniya Nuhu Gidado ya aike wa gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, yana shaida masa ajiye mukaminsa na mataimakin gwamnan nan take.

Tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana cewar ya kamata ne ya kasance har karshen wannan wa’adin, amma a sakamakon wasu dalilai ya yanke shawarar sauka daga matsayin nasa.

Ya bayyana cewar, ci gaba da kasancewarsa a ofishin hakan tamkar rashin yi wa kansa adalci ne, don haka ne ya zabi barin ofishin.

Gidado ya ci gaba da cewa tun a ranar 19, ga watan Afirilun 2018, ne ya fara tunanin ajiye wannan matsayi.

Gidado ya gode wa gwamna Abubakar da kuma jama’ar jihar Bauchi  bisa ba shi dama a matsayin mataimakin gwamnan jihar na tsawon lokaci.

Tun da fari, Nuhu Gidado ya fara ne da nuna godiyarsa  bisa yadda gwamnan jihar Bauchi ya ba shi damar zama mataimakinsa na tsawon lokaci, ya yi bayanin cewar ya kammala yanke shawararce a kashin kansa domin fuskantar wata rayuwar ta daban.

Gidado ya bayyana cewar tun da farko ma, shi ya so ne a yi tafiyar nan karo na farko ne kawai da shi, don haka ne kuma ya ga dacewar ajiye wannan mukamin gami da fuskantar wani abin na daban.

Sai dai kuma, ga dukkan alamu kallo ya koma sama bayan ajiye mukamin da mataimakin gwamnan ya yi inda magoya bayan bangaren gwamnan jihar suke ganin murabus din nasa “ta fi nono fari”.

A hirarmu da wakilinmu ya yi da da babban mai tallafa wa tsohon gwamnan jihar Bauchi kan hulda da ‘yan jarida, Yakubu Adamu ya bayyana cewar a sakamakon gaza yin adalci wajen tafiya kafada-kafada da mai gidan nasu ne ya sabbaba shi yin murabus a kashin kansa.

Ya ce, “Yin murabus din tsohon mataimakin gwamnan jihar ya bayar da takardar ajiye aikin ne a bisa yadda ake daukansa a wannan tafiyar ne ya ga baida ce ba, ta yadda ake nuna masa wariya, hakan ne ya ga bai dace ba ya ci gaba da tafiya a irin wannan yanayin.

Mai tallafa wa tsohon mataimakin gwamnan ya kara da cewa, “Shi Injiniya Nuhu Gidado ya ga an ware shi a gafe ba a tafiya da shi, hakan ya sa ya ga mafita kawai ya ajiye aikin,” Kamar yadda ya shaida.

Ya ci gaba da cewa, a bisa rashin gamsuwar ne, a maimakon ya munufurci kowa gwamna ya ajiye ya yi gaba, “Yadda ake daukansa ne a wannan gwamnatin ya ga bai gamsu ba; sannan kuma ka sani a maimakon ka tsaya ka yi abin da bai kamata ba, ka zauna kana cin dunduniyar mutum gara ka ajiye masa aikinsa,”

“In ka lura ai shi tsohon mataimakin gwamnan ya yi takara da wannan gwamna mai ci a zaben fid da gwani na APC,” Kamar yadda ya shaida.

Sai dai kuma Alhaji Yakubu ya karyata batun nan da ke cewa mataimakin gwamnan ya ajiye mukamin nasa ne a bisa sha’awar da yake da ita na tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2019 da ke tafe da cewar babu gaskiya a ciki, “Sam babu gaskiya kan wannan batun,” in ji shi

A takardar manema labarai da suka fitar daga fadar jihar Bauchi, gwamnan ya amince wa mataimakinsa kan wannan murabus din.

Gwamnan ya amince da ajiye aikin mataimakinsa din ne sanarwar manema labarai wadda Kakakin gwamnan jihar Ali M. Ali ya sa wa hanu gami da raba wa manema labarai a jiya.

Ya ce “Gwamnan ya amince da murabus din Injiniya Nuhu Gidado a matsayin mataimakin gwamna, gwamnan yana kuma yi masa fatan alkairi a rayuwarsa ta gaba,” In ji Ali.

Gwamnan ya misalta hazakar da Nuhu Gidado ya nuna a lokacin da ke bakin aikinsa a matsayin wani mutumin da ya yi kokari wajen ci gaban jihar, ya bayyana cewar tabbas

Gidado ya cancanci jinjina da yabo a bisa kokarinsa.

Haka kuma, gwamnan ya nuna godiyarsa gaya bisa nuna halin kwarai da tsohon mai mukami na biyu a jihar ya nuna a cikin wasikarsa ta ajiye aikin.

Gwamnan ya ce, “Mun amshi wasikar ajiye aiki na mataimakina Injiniya  Nuhu Gidado. A madadin dukkanin jama’ar jihar Bauchi, ina gode masa a bisa hazakarsa da kuma gudummawar da ya bayar a lokacin da ke ofis,”

Gwamna Abubakar ya bayyana cewar har zuwa yanzu, Gidado yana da kima da mutunci a gwamnatinsa hade da jam’iyyar APC a jihar da ma kasa.

“Ina masa fatan alkairi a rayuwarsa ta gaba. Ina kuma fatan zai ci gaba da ba ni goyon baya domin samun nasarar gudanar da aiki yadda ya dace,” In ji gwamnan jihar.

A hirarsa da wakilinmu ta wayar tarho, Kakakin jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Yayanuwa Zainabari ya bayyana cewar basu sha mamaki kan wannan lamarin ba, yana mai cewa ya kamata ne ma a ce tuntuni Gidado ya dauki wannan matakin domin fita da mutuncinsa “Mu ko kadan wannan lamarin bai ba mu mamaki ba, saboda shi mataimakin gwamnan idan ka duba tarihinsa shi ya fito ne daga babban gida, ya san kima, ya kuma san mene ne ya sa ya amshi mataimakin gwamna domin ya taimaki jama’an jiharsa. Amma yau tun da ya fahimci gwamnati ba ta sa ciyar da jama’a gaba ba gwamma da ya ajiye,”

“A hakan ma ya makara, ya kamata ne tun a shekarar farko da ta biyu ta gwamnatin nan ya ajiye mukamin nan a matsayinsa na dan babban gida,” Kamar yadda ya shaida.

Haka kuma wakilinmu ya tuntubi Kwamared Sabo Muhammad babban mai tallafa wa gwamnan jihar Bauchi kan ilimi da fadakar da al’umma don jin ta bakinsa kan wannan lamarin, ya ce  tun ran gini tun ran zane “Komai da ka gan shi a rayuwa tun ran gini tun ran zane, kuma komai da ka ganshi na rayuwa mukaddari ne. yau shi ne Allah ya kaddara cewa shi mai girma tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi Injiniya Nuhu Gidado zai bar aiki da gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin mataimakinsa,”

Dangane da hasashen kasancewa musu karfen kafa ga tafiyar gwamnatin, ya ce “cikin yardar Allah ba mu ga wannan ba. Babu wata matsalar da hakan zai shafi gwamatin M.A,” Kamar yadda ya shaida.

Shi kuma wani jigo a tafiyar APC a jihar Bauchi Sani Shehu (Sanin Malam) wanda shi ma kwanan nan ya ajiye mukaminsa a matsayin mai tallafa wa gwamna kan ayyuka na musamman ya ce tabbas akwai rashin adalci a cikin tafiyar gwamnatin, ya yi bayanin cewar dukkanin yaron da ya hana mamansa barci tabbas shi ma ba zai rintsa ba “Billahillazi La’ilaHaillahuwa duk dan da ya ce uwarsa ba za ta yi barci ba, shi ma zai kwana kuwa bai rintsa ba, ina kuma mai tabbatar maka cewar gwamna, imaninmu mutanen Bauchi sai dai mu yi fatan Allah ya jikanmu Allah ya sauwake mana, amma Allah ya kawo mana shugabanni na gari,” In ji Sanin Malam.

LEADERSHIP A Yau Juma’a ta labarto cewar kawo yanzu dai jihar Bauchi ta dauki dumi, domin kuwa wannan labarin ajiye aiki da mataimakin gwamnan ya yi ya bullo da wasu ababen da suke boye, inda wasu ke ganin hakan ne ya dace a yayin da wasu kuma suke ganin bai kamata ya yi wa gwamnan hakan a daidai wannan lokacin ba.

Idan ba ku mance ba, wannan dai ba shi ne karo na farko da masu mukamai a gwamnatin M.A ke watsar masa da mukaminsa su kama gaba ba, an samu kwamishina da ya ajije kujerarsa, haka kuma an samu masu bayar da shawara da kuma mai rikon mukamin mataimakin shugaban karamar hukuma, wasu na ganin hakan a matsayin lallai akwai matsala a gwamnatin jihar, inda wasu kuma ke cewa kitson ne aka yi da kwarkwata a ciki.


Advertisement
Click to comment

labarai