Connect with us

LABARAI

Yau Aka Yi Babban Taron LEADERSHIP Na Shekara

Published

on


A yau ne za a gabatar da babban taron shekara-shekara na Kamfanin LEADERSHIP.

Taron wanda aka saba gudanar da shi duk shekara, zai gudana ne a Babban Dakin taron Cibiyar ‘International Conference Centre (ICC)’ dake Babban Birnin Tarayya Abuja.

An assasa babban taron da kuma bayar da lambar yabo ne domin Rukunan Kamfanin Jaridun LEADERSHIP ya yaba tare da karfafa gwiwar wasu zakakurai da suke tallafawa ci gaban al’umma walau a kamfanoni masu zaman kansu ko a vangarorin gwamnati.

A na zavo wadannan zakakurai ne daga cikin wadanda suka nuna bajinta a shekarar da ta gabaci na Babban Taron.

Babban taron na wannan shekarar an yi mishi take da Binciken Hanyoyin Samar Da Kudaden Shiga Ga Jihohi.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai zama babban bako na musamman a wurin taron, kuma zai gabatar da kasidar gabatarwa. Sannan kuma tsohon Gwamnan Jihar Kuros Ribas, Donald Duke ne zai zama Babban bako mai jawabi.

Babban Manajin Daraktan Rukunan Kamfanin LEADERSHIP, Alhaji Abdul Gombe ya tabbatar da cewa, Etsu Nupe ne zai kasance Uban taron. Sannan kuma gwamnonin jihohi da dama za su halarta a wannan shekarar.


Advertisement
Click to comment

labarai