Connect with us

LABARAI

’Yan Boko Haram 700 Sun Shirya Mika Wuya –Gwamnatin Nijeriya

Published

on


Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewar, fiye da mayakan kungiyar Boko Haram 700 Boko Haram suka nuna aniyarsu na mika wuya, a dai dai lokacin da gwamnatin take kara bayyana irin halin tashin hankalin da yakin da ahka shekara 9 ake gudanarwa ya shafi rayuwar mutanen dake zaune a yankin Arewa maso Gabas.

Ambasadan Nijeriya kuma wakili na dindindin a majalisar dinkin duniya, Tijjani Bande, ne ya bayyana wa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya cewa, mutane fiye da Miliyan 14.8 ne rikicin ya shafa. Ya ce, an tarwatsa mutane Miliyan 1.7, sun zama ‘yan gudun hijira, mafi yawan wadanda lamarin ya shafa kuma kananan yara ne da mata.

Mista Bande na jawabi ne a wahen wani tattaunawa a kan hanyoyin kare fafaren hula a yayin da ake gudanar da yaki da muggan makamai. Ya tabbtar wa kasashen duniya da cewa, shirin da gwamnatin Buhari ked a shi mai suna ‘The Buhari Plan’ zai kawo sauki matuka a yankin Arewa maso gabas inda ‘yan kungiyar Boko Haram ke cin karensu babu babbaka duk kuwa da matakai na soji da ake kai musu.

Kwamitin shugaban kasa a kan Arewa maso gabas ce ta, samar da tsarin ‘The Buhari Plan’ – tsari ne da aka shirya zai sake tsugunar da wadanda ta’addanci ya cutar a cikin shekaru 9 da aka yin a ci gaba da yakin da kuma farfado da garuruwan da yakin ya tarwatsa.

Mista Bande ya kara da cewa, an samar da tsarin “Social Protection Initiatibe” da “National Action Plan” domin aiwatar da cikakken tanaden tanaden da dokan majalisar dinkin duniya mai lamba 1325 (2000), an fitar da shi ne saboda kare fararen hula musamman mata da kananan yara daga cutarwar da dakarun Boko Haram suka yi wa jama’a.

“A kan haka, wadannan shirye shiryen zasu taimaka wa aiwatar da tsarin nan na ‘The Buhari Plan’, wanda ya fitar da tsari dalla dalla yadda za a samar da agaji da farfado da tattalin arzikin yankin Arewa maso Gabas da kuma sake tsugunar da wadanda suka tarwatse daga gidajen su.

“A halin yanzu muna hadin kai da kasshe makwabtanmu kamarsu Chad da Cameroon da Niger da kuma Benin, ta hadakar jami’an tsaro na “Multinational Joint Task Force” domin karya alkadarin kungiyar Boko Haram, wadanda ke harin mata da yara kanana”.

Tsarin “Buhari Plan” nada nufin cimma tsaftataccen yankin Arewa maso gabas da zai zama abin alfahari ga duniya baki daya a fannin farfadowa bayan fuskantar rikicin ‘yan ta’adda.

Ambasadan ya kuma kara da cewa, Nijeriya na daya daga cikin kasashen da suka rungumi tsarin nan na “Safe Schools Declaration” da aka kaddamar a garin Oslo, inda akayi alkawarin kare makarantu a yayin da ake fuskantar yaki tare kuma da kare manyan makarantu da jami’o’i daga fadawa amfanin ‘yan kungiyar Boko Haram a yayin yaki da makamai.

Miata Bande, ya kuma ce, wannan sanarwa ta kara karfafa Nijeriya a tsarin nan nata na “Nigeria’s national Safe Schools Initiatibe” da aka kafa a shekarar 2014, a matsayin martanin gwamnatin tarayya wajen samar da amintaccen yanayin gudanar da karatu.

Ya ce, wannan shirin, yana nuna kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaro ga mata da kananan yara a lokacin da ake yaki da makamai, domin samar dasu a yayi da ake yaki, ta yadda za a samu kare aukuwar yakin da sake gina garuruwar da yakin ya lallata.

Ambasadan ya kuma ce, “Ya kamata jama’a su sani cewa, an yi garkuwa da mata da kananan yara da yawan gaske, amma tuni aka kubutar dasu , sannan dukkan wuraren da ‘yan ta’adda suka mamaye an karbosu.

“abin da muke gani a yakin tabkin Chadi ya zama hujjar cewar, in har akwai karfin hali da taimakon kasashen waje za a iya murkushe ta’addanci.

“Haka kuma gwmnatin Nijeriya ta samar da wani shiri na musamman mai suna ‘Operation Safe Corridor’, domin tabatar da sake tsugunar da kuma sake mayar da ‘yan ta’adda cikin al’umma, musamman wadanda suka nemi mika wuya da radin kansu daga cikin mayakan Boko Haram zuwa ciki al’umma.”.

Ambasadan na Nijeriya ya kara da cewa, da yawa daga cikin ‘yan ta’addan sun mika wuya ga hukumomin sojoji da radin kansu yayin da fiye da 700 suka nuna aniyarsu na mika wuya.

Ya ce, gwamnatin Nijeriya ta dauki matakin kula da wadanda ‘yan Boko Haram suka cutar musamman ta hanyar fyade da cin zarafi da sauran laifukkan yaki.

Ya kuma bayyana cewa, wadanan matakan sun hada da samar da kayayyakin agajin gagawa da kudaden jari, ga masu sana’a da kumam bayar da tallafin karatu ga matasan yankin Arewa maso gabas.

“duk da kokarin da ake gudanarwa a matakin kasa, muna da cikakken sanin cewa, kare fararen hula a yayin yaki da makamai abu ne mai matukar mahimmanci, ba wai ga majalisar dinki duniya kadai har ma das aura kasashen duniya gaba daya.

“A saboda haka muna matukar bukatar agajin gamayyar kasashen duniya domin maganin matsalar.

“A kan haka muna mika jinjina ga sojojinmu da sauran masu ruwa da tsaki da sauran kungiyoyi a bisa kokarinsu na aiki tukuru domin tabbatar da tsaron fararen hula a yayin yakin da ake gudanarwa” inji Mista Bande.

 


Advertisement
Click to comment

labarai