Connect with us

LABARAI

Masarautar Isa A Sakkwato Ta Tara Kudin Zakka Naira Milyan Shida

Published

on


A hobbasar kwazonta na karba da kuma rarraba zakka ga wadanda suka cancanta, Masarautar Isa a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Gobir na Isa, Mai Girma Alhaji Nasiru Usman Ahmad II ta samu nasarar tara kudin zakka da wakafi wadanda adadinsu ya kama naira miliyan shida.

Mai Girma Sarkin Gobir na Isa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a fadarsa a yayin da yake bayani a wajen rarraba zakka da Gundumar Isa ta tara a kwarya-kwaryar bukin wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya jagoranta.

Haka ma Sarkin Gobir na Isa ya bayyana cewar Masarautarsa a Karamar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato ta tara buhun shinkafa 200 da shanu 16 da kuma tumaki da awaki 56.

“Masarautar Isa ta samu nasarar karbar gonaki uku a matsayin wakafi wadanda daga cikin su akwai gona mai hekta 10 da kuma mai hekta 3. Mun kuma samu wakafin fili wanda kudinsa ya kai naira milyan 2, 950 wanda akalla mutane 750 za su amfana.” In ji Sarkin.

A jawabinsa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya jinjinawa kokarin Sarkin Gobir na Isa kan kokarin da yake yi na tara zakka tare da yi wa al’umma hidima wanda ya bayyana a matsayin abin yabawa.

Shugaban na Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya, ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su ci-gaba da bayar da gudunmuwa sosai ga jami’an tsaro domin kara inganta sha’anin tsaro a yankin da ma kasa bakidaya domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki ya bayyana cewar a Hukumance za su ci-gaba da yin iyakar kokarinsu wajen kula da gonakin da aka samu a matsayin wakafi ta hanyar bayar da kulawar musamman domin ganin al’umma sun amfana.

Maidoki ya kuma kalubalanci mazauna yankin Isa da su kara tashi tsaye haikan wajen noman rani da na damana musamman saboda kasancewar Allah ya albarkaci yankin da kasar noma mai kyau.

Ya ce “Idan kuka rungumi sha’anin noman rani da na damina sosai to ba shakka wannan yankin zai kara samun wadatar abinci tare da samun zakka da wakafi mai yawa a nan gaba.” In ji Maidoki.

Tun da fari dai Sarkin Gobir na Isa, Alhaji Nasiru Usman Ahmad II ya bayyana godiyar Masarautarsa ga al’ummar yankin wadanda ke jajircewa wajen bayar da zakka da wakafi yadda ya kamata tare da rokon Ubangiji ya saka masu da mafificin alheri.


Advertisement
Click to comment

labarai