Connect with us

LABARAI

Zaben 2019: Kishin Al’ummata Ya Sa Na Fito Takarar Gwamnan Jigawa –Hajiya Elleman

Published

on


Kishin al’ummata da kuma ganin sun samu rayuwa mai kyau da inganci ya sa na fito neman tsayawa takarar gwamnan jihar Jigawa a zaben 2019.

Wannan bayani ya fito ne da bakin ‘yar takarar neman kujerar gwamnan jihar Jigawa a tutar jami’yyar SDP Hajiya Ramatu Sabo Elleman a lokacin da take zantawa da manema labarai kwanakin baya a Kano.

Hajiya Ramatu Sabo Elleman ta kara da cewa wannan neman takarar data fito sai da da shawarci ‘yanuwa da abokan arziki musamman matasan da suka fito daga wasu sassan jihar, wannan ya sa ba tare da bata lokaci ba ta amsa musu tun da Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya ga dama, kuma a wurinsa take nema.

Ta ce, matukar ta samu nasarar darewa kujerar gwamnan jihar Jigawa, tana da tsare-tsare da kuma manufofi masu kyau domin ciyar da jihar Jigawa gaba, musamman matasa maza da mata dake yankunan karkara domin sune suka fi bukatar neman tallafi daga gwanati.

Zata samar da wuraren koyar da sana’oin dogaro da kai tare da bayar da jari domin bunkasa sana’oi ga wadanda suke da sana’a.

Harkokin ilimi shi ma za a ba shi muhimmanci domin duk inda babu ilimi babu ci gaba, tare da bunkasa harkokin tsaro ta yadda ‘yankasuwa da masu zuba jari zasu ji dadin gudanar da harkokinsu ba tare da fargaba ba. Saboda haka sai ta yi kira ga duk mai son ci gaban jihar ya zo domin taimaka mata ga kaiwa ga nasara.

Yar takarar, wadda tana daya daga cikin tsofaffin daliban ta KASSOSA ta yi kira ga daukacin yan jam’iyyar ta SDP na jihar Jigawa dana kasa baki daya cewa, su mara mata baya domin kai wa ga nasara sannan kuma su tabbatar sun amshi katin zabe domin da shi ne mutum zai zabi shugaban da yake so ranar zabe su tabbatar sun zabi SDP a ranar zabe.

Daga karshe ta yi kira ga al’ummar musulmi dasu yi amfani da wannan watan na Ramadan mai albarka wajen yi wa kasar nan addo’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

 


Advertisement
Click to comment

labarai