Connect with us

LABARAI

’Yan Kasuwa Ku Sassauta Sai Allah Ya Sassauta Maku –Ustaz Nuruddeen

Published

on


Wani jigo a kungiyar makiya ta kasa miyetti Allah daga Jihar Yobe Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya kalubalanci masu cewar makiyaya ne ke aiwatar da dukannin kashe-kashen rayukan bayin Allah da ba su ji ba, basu gani ba a Jihohin tsakiyar Nijeriya da suka hada da Filato, Binuwai, Nasarawa da ma wasu Jihohin da suka hada da Adamawa, Taraba, Kaduna, Zamfara da Katsina da cewar zancen kawai ne.

Jigo a kungiyar ta Miyetti Allah ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da wakilinmu a garin Damaturu dangane da yadda wasu marasa son gaskiya akullum ke alakanta kashe-kashen da ake yi a Jihohin da aka ambata a baya da sunan makiyaya ne ke aiwatarwa.

Mai Aliyu Usman ya kara da cewar babu inda za a yi a ce makiyayi dake yawo da dimbin dukiyar dabbobi amma wai a ce shi zai dauki makami ya na kashe bayin Allah da kone dukiyoyinsu ai ka ga , ga duk ma’abocin gaskiya ya san abu ne da ba zai taba yiwu ba haka siddan.

Ya ci gaba da cewar, su fa makiyaya da aksarinsu musulmai ne sun san da cewar addinin musuluncin ya hana kashe ran dan adam haka siddan ai kuwa da kamar wuya a ce suna daukar makamai don aikata ta’assa.

Mai Aliyu ya ci gaba da cewar, lalle a wani lokaci dabbobi kan iya kubcewa a cikin dare ta je ta aikata barna a gonaken manona ba tare da sanin makiyayin ba amma daga bisani in an gano hakan akan zauna a sasanta ba tare da tada jijiyar wuya ba. To amma a ce makiyayin dake yawo da dukiyoyinsa da mata da ‘ya’yansa wai shi ne zai rika tada fitinar da zata haifar da rasa rayuka ai kaga akwai ja akai duk da cewar ba a taru an zama daya ba.

Don haka ina kalubalantar duk mutumin da zai ce maka ga makiyayi da dabbobinsa da mata da ‘ya’yansa tafe yana tada hankalin mutane da cewar hakan ba zai taba yiwuwa ba domin ai kwana-kwanan nan ‘yar manuniya ta nuna inda aka kama wasu matasa kusan su 10 dake shigar bultu dauke da bindigar kiran Ak 47 wadanda dukan ‘yan kabilar Tibi ne da wasu ke daukar dawainiyar don bata sunan makiyaya Fulani don kawai tsatsonsu ne ke mulkin kasar nan.

Ya kara da cewar mafi yawan hotunan da ma masu shafa kashin kajin ga makiyaya Fulani ke nuna basa nuna daga kan su ya zuwa kasa sai dai su rika nuna daga kafadunsu ya zuwa kasa to wannan ba munafurci bane?

Kuma a cewarsa abubuwan da ke faruwa a Jihohin Zamfara da Katsina da wasu sassan Birnin Gwari kada’an ga duk ma’abucin gaskiya ya san da cewar ba makiyaya bane ke tafka irin wannan ta’assa, barayine kawai ‘yan ta’adda da muke fatan Allah SWT Ya mana maganinsu.

Kan hakan ne sai jigon na kungiyar makiyaya ta kasa ya kirayi gwamnatin tarayya da hukumomin tsaron kasa da kara kaimi dangane gano asalin masu aikata irin wannan ta’assa ta kashe-kashen rayukan mutane da masu rusa wutar wannan aika-aika don bukatar kansu don yin maganinsu ta yin hakan ne kawai zai kai ga kunyata masu yin yarfe ga Fulani makiyaya saboda kiyayya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai