Connect with us

LABARAI

Wadanda Ba Su Ci Zabe Ba Su Rungumi Kaddara –Bindow     

Published

on


Gwamnan jihar Adamawa Umaru Bindow Jibrilla, ya shawarci mambobin jam’iyyar APC musamman wadanda suka tsaya zabe ba su ci ba, da cewa ba fushe za su yi ba, hakori za su yi su hadakai domin ci gaban jihar da jam’iyyar APC.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwar manema labarai da kwamishinan yada labarai da tsare-tsare ta jihar Ahmad Sajoh, ya aikewa manema labarai a Yola, ta ce na yi wa daukacin ya’yan jam’iyyar fatan alheri.

Ta ce “APC mu abu guda ne, da wanda ya lashe zabe da wanda baici ba, duk nasarar namu ne jam’iyyarmu ta yi nasara, mu hada kai mu yi aiki tare domin tabbatar da nasaran jam’iyyar mu.

“na gode da hadinkan da shugabanni da mambobin jam’iyyar daga matakin gundumomi da kananan hukumomi, suka bamu lokacin gudanar da zabuka, muna fatan zaku ci gaba da bamu hadinkai da goyon baya haka.

“na yi farin ciki mkatuka da nuna halin dattako, da kaunar juna dama hadinkan da mambobin jam’iyya masu kada kuri’a suka nuna kafin da bayan zaben” inji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnan ya yabawa masu ruwa da tsaki a jihar, bisa jajirciwar da suka nuna, na ganin zaben ya gudana lami-lafiya cikin kwanciyar hankali, ba tare da an musguwa kowa ba, “abun farin ciki ne wannan kaunar juna da masu ruwa da tsaki da jama’ar Adamawa suka nuna”.

Ta ce, “a madadin mambobin jam’iyyar APC, muna yi wa kwamitin da uwar jam’iyyar ta turo ta gudanar da zaben barka, sun nuna kwarewa a lokacin gudanar da aikinsu, mun yaba musu matuka, da kaunar zaman lafiyar da suka nuna wa jiharmu” inji Bindow.


Advertisement
Click to comment

labarai