Connect with us

LABARAI

Tsintar Gawa Ta Tayar Da Hargitsi A Jos

Published

on


Gano gawar wani mutum da aka yi a kasuwar tumatur unguwar Farin Gada dake garin Jos ta jihar Filato da sanyin safiyar ranar Litinin ya tayar da hatsainiya, inda matasa suka shiga zanga zanga suna farfasa motocin jama’a masu zirga zirga.

Bayanai sun nuna cewa, Farin Gada, wata kasuwa a garin Jos dake ci a kullum inda ake siyar da tumatu da sauran kayan gwari, kasuwar na cika a kullum musamman a ranakun Litin da Alhamis da kuma Asabar.

Jami’in watsa labarai na rundunar sojojin “Operation Safe Haben” Manjo Adam Umar ya ce, an tsinci gawar wani matashi ne a bayan kasuwar Farin Gada ranar Litinin, ya kara da cewa, amma maimakon matasan su kai rahoto ga jami’an tsaro sai kawai suka shiga tayar da hankalin jama’a musamman masu motoci.

Manjo Umar ya kuma kara da cewa, tuni rundunar hadakar jami’an tsaron suka kwantar da hankali a yankin, ‘yan sanda kuma sun dauke gawar zuwa ofishinsu.

Da yake jawabi ga ‘yan jarida, shi ma, tsohon jami’in watsa labaran kasuwar, Mista Tasiu Kura, ya ce, ya zuwa karfe 11 na safe, harkoki sun kankama a kasuwar, an kuma kawo jami’an tsaro domin maganin sake faruwar tashin hankali.

 


Advertisement
Click to comment

labarai