Connect with us

LABARAI

Kayan Masarufi: Etsu Nupe Ya Ja hankalin ’Yan Kasuwa Kan Kara Farashi A Ramadan

Published

on


Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar wanda kuma shine shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Niger, yayi kira da ‘yan kasuwa cewar kada su yi amfani da watan Azumi na Ramadan kara farashin kayayyaki, domin kawai su samu riba.

Etsu Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin hutun karshen mako a fadarsa ta Wadada, lokacin da yayi taro da Limamai, Malaman addinin muslunci, da kuma wakilan ‘yankasuwa daban daban, saboda ya tunatar dasu amfaninsu a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan.

Kamar yadda Basarakenn ya bayyana ‘’ Wadanda suke amfani da wannan  na Ramadan saboda su kara farshin kayayyaki, ya kamata su kara yin tunani, su kuma ji tsoron Allah, kada su sa ‘yanuwansu maza da mata su fuskanci wata wahala’’.

Ya kuma ja kunnensu akan wa’azin da bai dace ba, inda ya kara  bayanin cewar duk wani wa’azin da bai dace ba, yana iya rashin jituwa, tsakanin al’umma, ko dai lokacinn Azumin, ko kuma bayan shi.

Ya ci gaba da bayyana cewar duk wani wa’azin da ya kamata ayi wannan lokaci, da akwai bukatar, a fi mayar da hankali akan zaman lumana tsakanin al’umma, ba wai ayi wani abin da zai kawo rarrabuwar kan jama’a ba kamar dai yadda Etsu Nupe ya ce’’.

Basaraken ya kara tunatar da al’amarin zaman lumana tsakanin al’umma, shine abinda ko wanne lokaci ace ana yin hakan, domin samar da zaman lafiya, hadin kai, da kuma ci gaba na al’ummar Nupawa, jihar Niger, da kuma Nijeriya.

Shima da yake jawabi a madadin wadnda suka halarci taron babban Limamin Bida Sheikh Adamu Liman –Yakatun, ya yi garagadi ga kowa, akann a rika jin tsoron Allah koda yaushe, da kuma tuna cewar da akwai ranar karshe.

Ya kuma yi kira da masu hannu da shuni dasu taimaka wajen ciyar da masu karamin karfi, saboda hakan zai rage masu irin wahalar da suke sha,lokacin Azumin watan Ramadan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai