Connect with us

LABARAI

JAMB Ta Ware Ranar 26 Ga Mayu Don Sake Jarrabawa Ga Sama Da Dalibai 12,000

Published

on


A ranar lahadin da ta gabata ne hukumarJAMB ta sanar da cewar ta ware ranar ashirin da shida ga watan Mayun 2018 don sake zana jarrabawa ga samada dalibai 12,000 a daukacin fadin kasar nan.

Mai yada labaran hukumar Dakta Fabian Benjamin,ya sanar da hakan a hirar sa da kafar dillancin labarai ta kasa a Abuja.

A cewar Benjamin, sama da dalibai 12,000 ake sa ran za su zana jarrabawar a wasu ‘yan cibiyoyin dake fadin kasar nan.

A cewar sa, daliban da zasu zana jarrabawar sune wadanda ba’a iya daukar bayan su ba a lokacin da aka zana jarrabawar tunda farko a watan Maris.

Ya kara da cewar, harda kuma sauran daliban da har yanzu ba su samu ganin sakamakon jarrabawar su tun lokacin da aka zana jarrabawar a cikin watan Maris har zuwa yau kuma ba’a kama su a cikin magudin jarrabawa ba.

Ya kara da cewa, jarrabawar ta kuma hada da waddanda ba su iya gurza takardar su ba kafin zana jarrabawar da kuma wadanda ake soke sakamakon jarabbawar cibiyoyin da suka zana jarrabawar su saboda zargin tabka magudin jarrabawa.

A cewar sa, akwai cibiyoyin da aka soke samakon jarrabawar su saboda zargin an tabka magudin jarrabawa, amma hukumar bata iya gano daliban da suka tabka magudin jarrabawar ba.

Ya sanar da cewar, amma daliban da aka kama su dumu-dumu akan tabka magudin jarrabawa da kuma cibiyoyin da aka tabka magudin tuni, hukumar ta yanke sharar baza su shiga sake zana jarrabawar da za’a yi ba.

Ya shawarci daliban da ya kamata suzo sake zana jarrabawar dasu gurza takardun su daga ranar 21 ga watan Mayu.

In ba a manta ba hukumar ta yi alkawarin cewar zata sake bari daliban su zana jarrabawar wadanda suke da kwakkwarar hujja.

 


Advertisement
Click to comment

labarai