Connect with us

LABARAI

Bayan Watanni Uku, Majalisar Dattawa Ta Karbi Rahoton Taron Tsaro Na Kasa

Published

on


A ranar Talata ne Majalisar Dattijai ta karbi rahoton taron samar da tsaro na kasa da aka yi a tsakanin ranar 8 zuwa 12 ga watan Fabrairu.

Shugaban Kwamitin Majalisar ne kan sake duba yanayin tsaro a kasarnan, Ahmed Lawan, ya mika rahoton.

Sakamakon matsalar tsaro da ke ta kara lalalcewa ne a kasarnan, aka shirya taron da nufin samar da dama ga duk shugabannin kasa domin nemo hanyar warware matsalolin na tsaro.

Amma kwamitin da aka kafa domin ya duba yanayin tsaron kasarnan a halin yanzun, ya kasa mika rahoton na shi bayan watanni ukun.

An kafa kwamitin ne sakamakon kashe-kashen sabuwar shekara da aka yi a Jihar Benuwe da wasu sassan Nijeriya.

Majalisar ta sha bayyana rahoton a matsayin mafita ga matsalar tsaro na kasarnan.

A lokuta da yawa, Shugaban Mjalisar, Bukola Saraki, ya yi ta neman rahoton.

 


Advertisement
Click to comment

labarai