Connect with us

LABARAI

Batun Mallakan Dala Milyan 15: An Sami Tsaiko A Shari’ar Da Patience Jonathan Ke Yi Da EFCC

Published

on


Rashin halartan kotun da Mai Shari’a Mohammed Idris, na babbar kotun tarayya da ke Legas bai yi ba a ranar Talata, ya kawo tsaiko a ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi tsakanin Uwargidan tsohon Shugaban kasa Jonathan da kuma hukumar EFCC, inda take kalubalantar umurnin kulle mata asusun ajiyar nata da hukumar ta yi.

An ce Alkalin yana halartan wani taro ne, sai aka daga sauraron shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Yuni.

Tun a shekarar 2016 ne Patience Jonathan ta shigar da karar, inda take kalubalantar hukumar ta EFCC da bayar da umurnin kulle mata wasu asusun ajiyarta guda hudu a Bankin Skye Bank, wanda suke shake da jimillan dala milyan 15.5.

Cikin wadanda ta shigar a cikin karar sun hada da, Bankin na, Skye Bank da wani tsohon mai taimaka wa Shugaba Jonathan, Waripamo-Owei Dudafa.

Har ila yau, ta shigar da wasu kamfanoni hudu cikin karar masu suna, Pluto Property and Inbestment Company Ltd; Seagate Property Debelopment and Inbestment Company Ltd; Trans Ocean Property and Inbestment Company Ltd; da Abalon Global Property Debelopment Ltd.

Duk da cewa, an bude asusun ajiyan ne da sunan kamfanoni hudu masu alaka da Mista Dudafa, Uwargidan ta Jonathan, ta shigar da karan ne tana ikirarin cewa kudaden nata ne.

A lokcin da aka kira shari’ar ranar 2 ga watan Mayu, Ifedayo Adedipe, ne ya halarci zaman a madadin wacce take karar, sa’ilin da, Nnemeka Omewa, ya halarta a madadin hukumar ta EFCC, Lanre Ogunlesi, kuma ya halarta a madadin wanda ake kara na biyu.

Lauyan wanda ake karar ya shaida wa kotun cewa, Lauyan EFCC ya nemi a daga shari’ar domin ya samu shigar da sabbin tuhuma, wanda ya ce ba sanar da shi hakan ba.

Sauran Lauyoyin ma suka ce duk ba su sami sanarwan hakan ba.

A lokutan baya dai, har shaidu sun fara bayar da shaidan su.

 


Advertisement
Click to comment

labarai