Connect with us

LABARAI

An Gudanar Da Zaben Shugabannin Kungiyar REATAN Ta Kasa

Published

on


Kwanakin baya ne aka gudanar da zaben shugabannin kungiyar masu motocin sufuri ta kasa “Road Transport Employers Associations of Nigeria REATAN.” an gudanar da zaben ne a babban birnin tarayya Abuja, inda aka samu da dama daga cikin ‘yan kungiyar suka halarta daga jihohin tarayyar kasar nan gaba daya, an yi zaben lafiya an kuma ta shi lafiya ba tare da wani hatsaniya ba.

Wanda aka zaba a matsayin shugaban kungiyar na kasa shi ne Alhaji Musa Shehu, wanda wannan zaben shi ne karo na biyu da sake zaben shi amatsayin shugaban kungiyar.

Da yake tsokaci game da sake zaben Alhaji Musa Shehu karo na biyu, jami’in ladabtarwar kungiyar na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Alasan Majiya, ya nuna farin cikinsa a bisa gaggaurumar nasarar daya samu.

Ibrahim Alasan Majiya, ya ce babu shakka Musa Shehu, shugabancin daya aiwatar a baya ya kawo wa kungiyar gagarimin ci gaban da ake bukata, musamman yadda ya hada kan ‘yan kungiyar na kasar nan sannan har ila yau ya daidaita kungiyar REATAN da sauran kungiyoin sufurin motoci dake fadin kasar nan .

Daga nan shugaban kungiyar na kasa ya nusar da ‘yan kungiyar muhimmancin hada kai da jami’an tsaron kasar nan domin samun zaman lafiya da fahimtar juna, Majiya ya ce, kar amanta kungiyar na samar da aikin yi ga al’umma musamman matasa tare da bayar da haraji da gwamnatoci.

Wani abu kuma da shugaban na kasa ya ke aiwatarwa shi ne samar da katafariyar sakateriyar kungiyar a Abuja wanda nan gaba kadan aikin zai kamala.

Kwamared Ibrahim Alasan ya yi amfani da wannan dama da kira ga ‘yan kungiyar na kasa dana jihar Kano dasu tabbatar sun bai wa shugabancin Musa Shehu hadin kai da goyon baya domin kai wa ga samun nasarar da ake bukata. Ya sake yin amfani da wannan dama da jinjinawa shugabancin kungiyar na jihar Kano, a karkashin shugabancin Kwamared Mustafa Jibirin game da yadda yake kokarin ciyar da kungiyar gaba tare da hada kan ‘yan kungiya ako da yaushe.

Daga karshe ya yi kira ga ‘yan kungiyar ta jihar Kano, dasu kara yi wa kungiyar biyayya da kuma da’a tare da tayata addu’a na fatan Allah ya kara baiwa kasar nan zaman lafiya da karuwar arziki


Advertisement
Click to comment

labarai