Connect with us

LABARAI

2019: Obasanjo Ya Ziyarci Shugaban Kungiyar Yarbawa, Fasoranti A Akure

Published

on


Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya kai ziyarar bazata ga shugaban kungiyar kabilar yarbawa (Afenifere), Mista Reuben Fasoranti, a garinsu Akure bayan shekaru 20 da yin irin wannan ziyarar.

Taron da aka gudanar a sirrince na tsawon mintina 30 ana kyatatta zaton yana da dangantaka da babban zaben 2019 da yadda ‘yan kabilar yarbaka zasu fuskaci zaben a dunkulensu.

Mista Obasanjo, wanda ginshiki ne a jam’iyyar ADC kuma shi ya kirkiro kungiyar nan mai suna CNM, ya isa gidan Mista Fasoranti da misalign karfe 3:03 na rana inda wasu jigajigan jam’iyyar ADC da sauran masu ruwa da tsaki suka tarbesa.

Bayan taron Mista Obasanjo, ya ki amsa tambayoyin ‘yan jarida akan ko ziyarar nasa tana da alaka da harkar siyasa.

“Shin da ba zai iya ziyartar ubansa a kowanne lokacin daya ga dama ba?

“Shin ina da bukatar neman izininku kafin in kawo wa uba na ziyara? Wai ma ta yaya wannan ziyarar ya shafe ku gaba daya? Inji shi.

Cikin wadanda suka rufa wa Mista Fasoranti baya a taron sun hada da wasu daga cikinn shugabannin kungiyar kamarsu Seinde Arogbofa sakataren kungiyar da Cif Sola Ebiseni da Kole Omololu da kuma Femi Aliko, inda suka ce lalai taron ya yi matukar armashi.

Shugaban kungiyar Afenifere ya ce, Obasanjo ya kawo masa ziraya ne, yana kuma gode masa a bisa kokarin da yake yi na hidima ga Nijeriya musamman yankin Yarbawa.

“Ya zo ne saboda yana mutunta abkantakar dake tsaninmu” in ji shi.

Mista Fasoranti ya kuma musanta cewar, sun tattauna game da harkar daya shafi zaben shekarar 2019.

Sai dai, ya nuna goyon bayansa game da wasikun da Obasanjo ya rubuta wa shugababMuhammadu Buhari in da yake korafi game kashe kashen da Fulani keyi a sassan Nijeriya da kuma yaki da rashawar da a keyi wannad ake fuskantar bangare daya kawai.

“Muna matukar goyon baya, bamu amince da yadda ake gudanar da mulkin ba, gaba daya bamu amince ba” inji shi.

Mista Fasoranti, ya kuma ce, basu tattauna a kan sabon jam’iyyar siysar nan ta ADC ba, amma ya ce, yana matukar goyon bayan yin wata hadaka mai karfi da zata kwace mulki daga hanun jam’iyyar APC a zaben shekarar 2019.


Advertisement
Click to comment

labarai