Connect with us

LABARAI

Zaben Shugabannin Jam’iyyar APC A Jihar zamfara Ya Zo Da Sabon Salo

Published

on


Zaben shugabanin jam’iyyar APC na jihar Zamfara ya zo da abin mamaki domin kuwa an kwashe mintoci ana yamutsa gashin baki tsakanin tsohon gwamna Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura da Gwamna Abdula”Aziz  Yari wajan cimma, shugaban jam’iyar ya mutsa gashin bakin da ya jawo canza dan takarar shugaban na jihar an take sannan aka koma raha.

A filin taron ne a ka tabbatar da cewa,  dan takarar shugaban jam’iyyar na jihar Zamfara shi ne Alhaji Hon. Lawali Liman kwamshinan lafiyar na jihar.

Shugaban zaben wanda uwar jam’iyyar ta kasa ta turo,Alhaji Umaru Danbo ya bayyana cewa a dokar zaben jam’iyyar APC a kwai zaben na saka kuria da kuma na daga hannun na aminta ,na daga hannu na cewa kuna so sai a amsa da cewar an yarda, ta haka aka gudanar da zaben gaba daya.

Nan take shugaban dake gudanar da zaben ya umarci, sakataren sa Mista Chinedu ya karanto duk ‘yan takaran dake da mukamai, su talatin da bakwai (37) da kuma na datawan jam’iyyar da dai sauransu.

Ya kira sunan ‘yan takaran duka masu kada kuria suka aminta da sabbin shugabannin, a sabon tsarin, Hon Lawali Liman Kaura ya zama sabon shugaban jam’iyyar na jihar Zamfara sai Alhaji Musa Mallaha a matsayin mataimakin shugaba sai kuma Alhaji Musa Sani Molo ya zama Sakataren jam’iyyar da Alhaji Babangida Anka sai kuma Jami’n hulda da jama’a na jam’iyyar ya fada hannun Alhaji Shehu A. Isah da mataimakinsa Samaila S. Fawa (Kwanka), sai shugabar mata ta jihar wanda Hajiya Jmmai Wakili ta samu.

Sai kuma shugabani na yankin ‘yan Majalisar Datawa Zamfara ta tsakiya, shugaban shi ne Alhaji Sani Mayanci sai kuma na Zamfara ta yamma inda Alhaji Aliyu Mai Kwarya Gumi ya samu, sai kuma shugaban Zamfara ta Arewa inda Alhaji Abdullahi Ja’o zai shugabanta.

A jawabin Gwamna Yari a wajen zaben, ya nuna godiyarsa ga dukkan ‘yan jam’iyyar APC da suka hadu don gudanar da zaben da kuma musayar miyau da akai tsakanin ‘yan jam’iyyar, yana mai cewar, sai ayi hakuri domin kuma haka jam’iyyar ta gada.

Shi ma anasa jawabin, sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar Hon Lawali Liman ya bayyana godiyarsa ne ga Allah a kan wannan mukamin daya samu, ya kuma dauki alwashin tafiyar da jam’iyyar yadda ya kamata.

 


Advertisement
Click to comment

labarai