Connect with us

LABARAI

Na Samu Dimbin Darussa Zama Na A Gidan Yari –Obasanjo

Published

on


Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce, tsarewar da marigayi shugaban gwamnatin mulkin Soja, Janar Sani Abacha, ya yi ma shi ta kasance alheri a gare shi ta wani fannin, domin kuwa a cewar shi, hakan ya kwakkwafa tunanin sa a fannoni da dama, wanda hakan ya taimaka ma sa a lokacin da ya shugabanci kasarnan.

Ya fadi hakan ne kuwa lokacin da yake magana wajen bude taron farko na, ‘ASIS International, ASIS 206 Lagos Annual Leadership Retreat,’ wanda aka yi a dakin karatu na, ‘Olusegun Obasanjo Presidential Library, da ke Abeokuta.’

Taron wanda kungiyar ta ASIS ta shirya, an yi shi ne da nufin samo hanyoyin za su tattaro dukkanin sassan tsaro na kasarnan waje guda.

Ya ce, “Zama na na gidan Yari, ya amfanar da ni. A gaskiya hakan ma ya taimaka mani wajen cimma nasarorin da na samu lokacin da nake shugaban kasa.

“Duk da cewa, ba wanda ke fatan zuwa gidan Yari, amma zama na a gidan Yarin ya sanya na koyi abubuwa masu yawa, na kuma iya shagaltar da kaina da abubuwan da suka amfane ni. Na rubuta littafai har hudu lokacin da nake a gidan Yarin, a maimakon na yi zaman banza ba tare da aikata komai ba, da zai amfane ni.

“A lokacin ina da tabbacin mutumin da ya jefa ni a gidan Yarin ba zai taba fitowa da ni ba, ina kuma da tabbacin watarana zan fito daga gidan Yarin. A gaskiya zama na na gidan Yari ya yi matukar amfanan rayuwata.”

Ya nu na goyon bayansa na yunkurin da ake na kafa tafiyar da za ta kusanto da sassan tsaro masu amfani da kaki da kuma na farin kaya, domin magance barazanar tsaro a kasarnan.

Obasanjo, wanda a zamanin mulkin sa ne a shekarar 2005, ya mayar da jami’an tsaro na NSCDC, daga halin da suke a baya na wasu masu aikin sa kai zuwa wannan halin da suke a kai yanzun na wani sashe na musamman na jami’an tsaro na farin kaya, ya ce, shi bai ga wata matsala kan daukaka matsayin na NSCDC, musamman na mayar da su daga masu zaman kansu zuwa matsayin kwararru masu yi wa kasa aiki.

Amma sai ya yi gargadin cewa, duk wani yunkurin da za a yi a kan hakan, ya wajaba a sa ido a kansa sosai, sannan kuma a gabatar da shi ga Majalisun kasa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai