Connect with us

LABARAI

Matar Gwamnan Bauchi Ta Raba Buhun Suga 5 Ga Masu Azumi A Bauchi

Published

on


A ranar Asabar ne matar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta raba wa al’umman unguwar Inkil da ke cikin garin Bauchi kayyakin Azumi domin tallafa musu a cikin watan Ramadana.

Kayyakin da matar gwamnan ta raba wa mabukata sun hada da buhun suga guda biyar kacal (5), katan-katan na manja da mangeda 5, yadunan zani guda 50 hade da buhun shinkafa guda 10 domin taimaka musu hade da rage musu wahalhalun rayuwa a watan Ramadan.

Hadiza ta yi rabon ne a wajen da mata ke gudanar da tafsirin Alkur’ani mai girma a unguwar Inkin da ke cikin Bauchi.

Da take jawabi a wajen rabon kayyakin, uwar dakin gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta bayyana cewar hakan na daga cikin yunkurinta na tallafa wa marasa shi ne a cikin wata mai alfarma.

Ta bayyana cewar irin wannan tallafin tana gudanar da shi ne a kowace shekara, da zimmar taimaka wa dukkanin matan da suke fadin jihar Bauchi, tana mai bayanin cewar irin wannan tallafin ta gudanar da irinsa a shekarar da ta gabata a kauyen Bada Romo.

Ta ce, tana bayar da tallafin ne domin matan su goyi bayan gwamnatin mijita a kokarinsa na ganin ya inganta rayuwar jama’an da suke jihar.

Hadiza ta ce, gwamna, mijinta ya yi kokari sosai wajen gudanar da kyawawan aiyukan ci gaba kamar su shimfida titian a sassa daban-daban na jihar domin jin dadin jama’an da suka yi umumu suka zabeshi.

Hadiza ta yi nuni da cewar wannan tallafin kamar kaddamarwa ne domin za ta zagayawa zuwa wasu kauyukan da suke jihar domin raba irin wadannan kayyakin buhun suga 5, shinkafa 10, yaduna 50 da manja da mangeda 5.

Da yake maida jawabinsa mai gundumar Inkil Alhaji Shehu Adamu Jumba ya gode wa matar gwamnan jihar Bauchi a bisa wannan gudunmawar da ta iya samar wa jama’ansa, yana mai addu’ar Allah baiwa gwamnatin mijinta nasarar kammala aiyukan da ta sanyo a gaba.

Ya bayyana cewar irin wannan tallafin zai taimaka wa mabukata gaya, yana mai godiya a bisa hakan.


Advertisement
Click to comment

labarai