Connect with us

LABARAI

Jihar Nasarawa Ce Ginshikin Nasarar Buhari A Mulki –Al-Makura

Published

on


Gwaman jihar Nasarawa Alhaji Umar Tanko Al-makura ya bayyana nasarar  samun shugabanci Muhammadu Buhari a yanzu haka ta samu ne ta dalilin tsayuwar tsayin daka da al’umman jihar Nasarawa suka yi ne a wajen zaben shekarar 2011.

Ya ce, alumman jihar Nasarawa masoya Shugaba Muhammad Buhari ne, shi ya sanya duk abin da yazo daga sama na jam’iyyar APC zaka ga an tafiyar da shi lami lafiya a jihar.

Gwaman ya kara da cewa, jam’iyyar APC a jihar Nasarawa yan uwan juna ne babu rikici na jam’iyyar a nan jihar shi ya sanya da aka zo zaben shugabannin Jam’iyyar APC tun daga mazabar gunduma zuwa kananan hukumomi zuwa jihar aka amince da wadanda suke kai cewa su ci gaba.

Gwamna Umar Tanko Al-makura ya fadi haka ne a ranar Asabar, wajen gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihar da kuma mika tuta ga wadanda suka yi nasarar lashe zaben fid da gwani na kananan hukumomi a jam’iyyar APC wanda za a gudanar da zaben gama gari a ranar Asabar mai zuwa,.

Gwaman ya kara da cewa, ya tabbatar jam’iyyar APC  za tayi nasara a wanan zaben saboda yanzu babu wata jam’iyyar hamayya a wanan jihar. Al’ummanr jihar Nasarawa sun hada kansu waje daya sun dunkule a Jam’iyyar APC. Ya kara da cewa, sirrin samun wanan nasara shi ne zaman Lafiya da gwamnatinsa ta samar a wanan jihar.

Yace, yanzu jam’iyyar APC ita keda sama da kasa saboda haka yana kira ga al’umman jihar Nasarawa dasu fito kwai da kwarkwata su kaddwa APC kuri’a a zaben dananan hukumomi sanan lokacin zaben 2019 su sake fitowa sunyiwa Jam’iyyar APC ruwan kuri’u daga sama har kasa . saboda shugaban kasa Muhammad Buhari na kune .

Shima dayake jawabi jagoran gabatar da zaben Jam’iyyar ta kasa da a yankin jihar Nasarawa Miata Mezogu E.Mezogu ya ce, ya yaba da yadda ake tafiyar da tsarin damukurdiyya a jihar Nasarawa saboda yadda yaga al’umman sun dunkule babu gaba da juna, ya ce, bai taba ganin tsarin siyasa mai kyau kamar yadda ya gani a jihar Nasarawa ba.

Ya kara da cewa, wanan sai ya tuna masa da siyasan shekarar 1999, yadda ya ga al’umman suna amincewa da junansu.

Ya ce, jihar Nasarawa ta bambamta da sauran jihohi da zaka tarar ana rigingimu wajen zabe amma gashi nan da suke da masu kada kuri’a kimanin 1775 daga mazabu 147 amma komai ya tafi a cikin tsari. Mista Mezogu ya kuma ce, ya tabbata an samu wanan tsarin ne ta yadda shugabannin keyin adalci ga alumma, da kuma yadda gwamnan jihar yake tafiyar da al’umma dama jam’iyyar.

Sanata Abdullahi Adamu tare da kakakin majalisa dokoki na jihar, Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi ne suka amince da ci gaban wadanan shugabannin jam’iyyar na tsawon shekara hudu a madadin sauran ‘yan jam’iyyar.


Advertisement
Click to comment

labarai