Connect with us

LABARAI

Al’umma Sun Yi Farin Ciki Da Nadin Baraden Kano

Published

on


An bayyana nadin da aka yi wa ministan harkokin cikin gida Janar mai ritaya Abdurrahman Bello Danbazau a matsayin Baraden Kano da cewa abin farin ciki ne ga dukkan al’ummar garin Takai. Shugaban karamar hukumar Takai, Barista Haruna Falali da dan majalisar jiha mai wakiltar yankin Kwamared Musa Ali Kachako suka bayyana hakan bayan nadin da aka yi wa Ministan a fadar Sakin Kano ranar Juma’a.

Barista Haruna Falali ya ce, ganin da irin gudummuwa da Janar Abdurrahman Danbazau yake bayarwa ga ci gaban yankin da jihar Kano da kasa baki daya tasa masarautar Kano ta zaboshi ta karramashi da wannan matsayi wanda ya zama karramawace ga dukkan al’ummar karamar hukumar Takai.

Shugaban na karamar hukumar Takai, ya yi fatan wannan sarauta zai dada karawa Ministan kaimi wajen ci gaba da jibintar al’amuran al’umma daya saba wanda hakan ta jawo masa girbar wannan babbar alkhairi na zama daya daga cikin ‘yan majalisar fadar masarautar Kano.

Shima dan majalisar jiha mai wakiltar Takai, Kwamared Musa Ali Kachako ya bayyana cewa, Abdurrahman Bello Danbazau ya cancanta da wannan matsayi dama abu ne da suke masa kyakkyawan zato akai kullum dan duk wanda ya tsaya ga taimakon al’umma, Allah zai taimaka masa dan haka wannan irin ayyukan da yake na alkhairi yake girba.

Kwamred Musa Ali Kachako ya ce, Danbazau mutum ne mai taimakawa al’umma da hada kanta da tabbatar da zaman lafiya wanda ya yi aikin soja har yakai ga babban mukami sannan ya yi ritaya kuma cancanta da kwarewarsa tasa Gwamnatin Buhari ta nada shi Minista, gashi yanzu kuma masarautar Kano ta nada shi a babban matsayi na Baraden Kano wannan abin alfahari ne ga duk al’ummar karamar hukumar Takai da jihar Kano baki daya.

A nasa bangaren, sakataren mulki na karamar hukumar Takai, Alhaji Sani Adamu Zuga ya ce, nadin da aka yi wa Abdurrahman Bello Danbazau wanda Ubane,yayane kuma danuwa ne ga al’ummar Takai suna farin ciki da shi domin an zabo kwarya data dace da gurbinta in aka yi la’akari da cewa, baya ga aikin soja masani ne na ilimi wanda har ya kai ga matakin Farfesa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai