Connect with us

LABARAI

Akidar Kwankwasiyya Na Kara Karbuwa A Fadin Kasar Nan

Published

on


An bayyana cewa akidar siyasar kwankwasiyya na ci gaba da yado da karbuwa a tsakanin al’umma sakamakon aikin alkhairi da Sanata Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya assasa na ci gaban jiharnan, Shugaban Dattawan Kwankwasiyya na karamar hukumar Dala, Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare ya bayyana haka a loacin yake tattaunawa da ‘yan jarida kwanakin baya.

Ya ce, su yan Kwankwasiyya kullum ba abin da suke gani sai alkhairi a tafiyar dan dada habaka take duk inda ka shiga loko da sako, ko kasuwa da wajen suna ko ta’aziyya da wajen kallon wasanni in suka je da jar hula muna ganin haba-haba da ake yi musu.

Ya kara da cewa, da yawa in yaje taro, inshi kadaine sai kaga mutum yazo ya ce, wannan abinda kuke kuna kan daidai kuma abu ne mai kyau, muma muna tare daku. In sun taho kamar su biyar suna tafiya sai kaji mutane suna tambaya ina ake taro nan da nan sai kaga an taru da yawa.

Dayyabu ya ce, duk inda dan siyasar da yake mu’amalar siyasa kyauta a tara mutane dubbai ba tare da an basu wani abu ba saboda akida, Sabanin wanda zasu bada kudi su tara mutane,amma ayi maka abu saboda akida, sai kwankwasiyya.

Alhaji Dayyabu ya ce, idan kudi suke so, sai subi Gwamnati suyi karya ayi musu abinda suke so, amma su ‘yan kwankwasiyya ba wannan ne a gabansu ba, me kayi a baya suke kallo da kuma me za a yi a gaba.

Yanzu misali kowa ya sani mutun nawa aka dauka aka tura kasashen waje karatu? Nawa aka dauka aiki? Yara nawa ake ciyarwa a makarantu a lokacin kwankwaso? Makarantu nawa aka gina abubuwa nawa aka kirkira dan anfanin al’umma, gasunan birjik ga da talakawa suka gani anyi musu, shi suke tunani aransu. Kuma sun ga tun daga wannan lokaci komai ya tsaya cak ba wani dauki, zancen ilimi sai dada tabarbarewa yake a yanzu sai dai ace Allah ya sawwaka.

Alhaji Dayyabu ya ce, ko yanzu Gwamnati ta gyara sunaso duk dan kishin kano yanaso,amma mai son kansa Gwamnati duk abinda tayi daidaine,shi kuma dan kwankwasiyya ra’ayinsa shine ya gani a kasa.

Shugaban Dattawan Kwankwasiyya na Dalan yayi nuni da cewa duk mai bibiyar abinda ya faro akan su da gwamnatin Ganduje,tun randa aka fara zaman sulhu .Gwamnoni suka hadu suka daidaita tsakanin jagoransu Kwankwaso da Ganduje kafin a baro Abuja yayi waya yace ya cire Doguwa daga shugaban jam’iyya in akabi abubuwanda ke faruwa duk abinda aka kulla yau da Ganduje akan sulhu gobe sai ya warwareshi.

Tunda aka ba wanda ya taba jin kwankwaso yace wani abu akan wannan matsalar koya gayawa Ganduje bakar magana ,amma shi kullum a cikin maganganu yake marasa dadi akansa.

Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare yace idan anaso a dinke baraka to kowane abu a ajiyeshi a muhallinsa to da kanta ma saita dinke,duk mai gaskiya a bashi ayi hakuri da juna ayi mu’amala .Amma idan ba’a ajiye kwarya a gurbinta ba zancen dinke baraka zai wahala.

Dayyabu yace su mutane su sukeda hukunci idan zabe yazo zasu duba wanene yayi musu abin kirki zasu saka masa,wanene kuma yayi sabanin haka kowa zai girbe abinda ya shuka.


Advertisement
Click to comment

labarai