Connect with us

LABARAI

2010 Zuwa 2015: Hukumomi Sun Tafka Ta’asa Lokacin Jonathan –Lai Mohammed

Published

on


Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa hukumomi 15 na gwamnatin tarayya ne suka ki su zuba Naira tiriliyan 8.1 a asusun gwamnatin tarayya daga shekarar 2010 zuwa 2015.

Ministan ya yi wannan bayanin ne jiya a garin Osogbo na jihar Osun yayin da yake kaddamar da wasu ayyukan raya kasa.

Alhaji Lai mohammed wanda ya wakilci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wurin taron, ya ce irin ta’asar da kamfanin bin diddigi na KPMG ya bankado ya zarce Naira Tiriliyan 1.34 da ma’aikata 55 suka sace a tsakankanin 2006 zuwa 2013.

“Kwanan nan, Gwamnatin Tarayya ta sanya a bi diddigin wasu hukumomin Gwamnati guda 15 (daga shekarar 2010 zuwa 2015). A nan ne aka bankado cewa wadannan hukumomin ba su zuba adadin kudi naira Tiriliyan 8.1 ga asusun gwamnatin tarayya ba, kamar yadda yake a ka’ida. Wannan ya nunka abin da ake zargin an sace daga shekarar 2006 zuwa 2015.” inji ministan

Ministan ya kara da cewa, ayyukan da wannan gwamnatin ta zartas, wanda ya hada da ayyukan da ya kaddamar a Osogbo (ciki har da wasu ire-irensa guda 52 a fadin kasar) da tuni an gama da su an shiga wasu ayyukan. Amma saboda matsananciyar ta’asar da barayin gwamnati suka tafka, dole ayyukan sun hadu da tsaiko.


Advertisement
Click to comment

labarai