Connect with us

LABARAI

Zaben APC: Shugabanin Jam’iyyar Sun Sake Lashe Kujerunsu A Bauchi

Published

on


A ranar Asabar din nan ne aka gudanar da banban zaben jam’iyya mai mulki wato APC a matakan Jahohi. Zaben na jihar Bauchi bai zo wa masu yi da ciwon kai ba, domin kuwa shugabanin da suke jan ragamar jam’iyyar tun da fari sune suka sake dalewa bisa karagar mulkinsu biyu bayan yin zaben ta hanyar amince masu su daura.

An gabatar da zaben ne a dakin wassani  na Multipurpose da ke Bauchi, inda kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi suka zo, a yayin da kuma zallar masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar ne aka basu zarafin zaben shugabanin jam’iyyar a matakin jihar.

An gabatar da kujeru 36 da suke karkashin jam’iyyar na jihar, inda mafiya yawansu koma dukkaninsu shugabanin APC ne wanda tun da fari ma sune, an amince musu domin su sake jan ragamar APC har nan da shekaru hudu masu zuwa.

Tun da fari shugaban kwamitin da ya jagoranci gudanar da zaben a jihar Bauhci Dakta Kabiru Ibrahim Matazu ya bayyana cewar kawo lokacin za su ka fara gudanar da zaben babu wani kujera da suka samu wani ya saye baya ga wadanda suke kai, don haka ne ya bayyana cewar a dukkanin kujeru da ofis-ofis guda 36 da suke karkashin jam’iyyar a jihar Bauchi wadanda suke kai sun ci babu hamayya.

Yana bayanin cewar dukkanin sabbin shugabanin sun cike dukkanin sharadu da ka’idodin da uwar jam’iyyarsu ta kasa ta fitar kan zaben.

Matazu ya bayyana cewar sun zo da dukkanin kayan gudanar da zaben kamar yadda aka umurcesu amma a sakamakon rashin samun masu hamayya da wadanda suka saya fom mutane day-day wanda sune jagororin APC tun da fari hakan ya bayar da damar sake basu zarafin ci gaba da jan mulkin APC.

Sabbin jagororin APC a jihar Bauchi sun hada da Alhaji Uba Ahmad Nana a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar Bauchi, shi kuma Muhammad Hassan ya ci gaba da kasancewa a matsayin mataimakin shugaba, Bako Hussaini Shira a matsayin sakataren jam’iyyar.

Sauran zababbun sune Murtala Ibrahim (Dan Malikin Botu) a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar a shiyyar Bauchi ta Kudu, Injiniya Zari Dogo mataimakin shugaba a shiyyar Bauchi ta tsakiya, sai kuma Abbas Turaki Jama’are a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar APC a Bauchi ta Arewa.

Hade da sauran kujeru da suka su kai 36, kujerun da suka rasu kamar na Kakakin Jam’iyyar an maye gurbinsa da wanda jam’iyyar ta aminta.

Da yake jawabinsa a wajen zaben sabbin jagororin APC na jihar Bauchi, Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullah Abubakar ya bukaci sabbin zababbun APC da su kara kaimi domin kawo wa jam’iyyar gagarumar nasara a zaben da ke tafe.

Ta bakinsa, “Ni kira a gareku bayan na taya ku murna da cewar kada ku zaci mun riga mun ci yaki, ina son na tabbatar muku yanzu ne yaki zai fara. Ba don komai ba saboda da mun yi kura-kurai a baya mu ‘ya’yan jam’iyyar APC, a lokacin da muka karbi ragamar mulki a shekara ta 2015, ‘yan adawarmu da suke sauran jam’iyyu da dama wallahi ko tari mai karfi basu iya yi.

Mune da kashin kanmu muka dinga cin dunduniyar junanmu a jam’iyyar APC har muka basu dama suna iya daga fuskokinsu a gansu a jihar Bauchi,”

Ya kara da cewa, “To yanzu salon tafiya ya canza. Mun zabeku zababbun sabbin shugabanin APC a dukkan matakai, saboda haka mu tare mu dukafa mu fara aiki haikan. Aikin da za mu yi yanzu ya fi aikin da muka yi a shekara ta 2014 da 2015. Ba don komai ba ko don hassadar dan adam. Yau mune a kan ragamar mulki, kasancewarmu a matsayin masu jan ragamar mulki babbar laifi ne a wajen masu hassada da mu,” In ji Muhammadu.

Gwamnan Bauchi ya ci gaba da cewa, ‘ya’yan jam’iyyarsu da suka fankare suna da sauran damar su dawo domin ya amshesu hanu biyu-biyu domin tunkarar zaben da ke gaba “’yan’uwanmu da suka fankare ina tabbatar muku har gobe ina daidai da in zauna su idan sun kawo kansu, har yanzu ina daidai da in rokesu mu yafe musu domin mu sake ci gaba da tafiya da su domin tafiya tsintsiya daya madaurinki daya,” In ji M.A Abubakar.

Makama Babba na Bauchi ya kuma shaida cewar gwamnatin APC a jihar Bauchi sai Allah sam-barka, domin kuwa kama daga kasa zuwa jiharsa APC ta taka gagarumar nasara, “Nan gaba kadan za mu sake kaddamar da wasu aiyukan da muka,” A ta bakin Makama.

Da yake nashi jawabin na godiya, sabon shugaban APC wanda zai sake shafe shekaru hudu a matsayin shugaban APC a jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmad Nana ya fara ne da nuna godiyarsa wa dukkanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a bisa amince masa da sake zabensa a matsayin shugaban APC a jihar.

Ya sha alwashin cewar zai zage damtse domin kawo wa APC gagarumar nasara a zaben da ke tafe na 2019.

Uba Nana ya bayyana cewar dukkanin wani tsari da aka fitar wajen yin zaben an yi wa kowa da kowa adalci, don haka ne ya bayyana cewar aiki ne a kan sauran zababbun da su tashi tsaye wajen yin aiki kafa-kafa domin kai APC mataki na gaba, ya kuma bayyana cewar sun samu darusa masu tulin yawa a mulkinsu na baya, don haka yanzu za su bi hanyoyin da suka dace domin kyautata jam’iyyar.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai