Connect with us

LABARAI

Manufarmu Shi Ne Tallafa Wa Matasa -Walin Fagachin Zazzau

Published

on


“Babban dalilin day a sa mu ka kafa kungiyarmu shi ne mu ga mun tallafa wa matasa maza da kuma mata, su sami damar ci gaba da neman ilimi da kuma samar ma su da sana’o’in dogaro da kai, da za su tallafa wa kansu su kuma tallafa wa al’umma a gobe’’.

Shugaban kungiyar ci gaban matasa, wato ‘KADA YOUTH DEBELOPMENT ASSOCIATION’, reshen jihar Kaduna, Alhaji Salisu Abdu, kuma Walin Fagachin Zazzau, ya bayyana haka ga Leadership A YAU, jim kadan bayan sun kammala taron da suka saba yi a Zariya.

Alhaji Salisu Abdu ya ce a bangaren ilimi, a shekara da ta gabata, kungiyarsu ta tallafa wa matasa 250, inda suka sami shiga Jami’ar Jihar Kaduna, da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da kwalejin kimiyya da fasaha ta tunawa da Nuhu Bamalli da ke Zariya da kuma kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Zariya.

Yanzu haka daukacin daliban da wannan kungiya ta tallafa ma su suka shiga kafafen neman ilimin da aka ambata, suna ci gaba da karatunsu ba tare da wasu matsaloli ba.

A game kuma da ayyukan dogaro da kai, Alhaji Salisu Abdu Walin Fagachin Zazzau ya ce, sun koya wa yara fiye da hamsin sana’o’in dogaro da kai a shiyya ta daya da shiyya ta biyu da kuma shiyya ta uku a jihar Kaduna. Zuwa yanzu kamar yadda ya ce, mafiya yawan matasan na ci gaba yin sana’o’in tare kuma da koya wa wasu matasan da suka je wajensu, domin neman sana’ar yi.

Wannan matakin da suka dauka, a cewar Walin Fagachin Zazzau, ya haifar ma su da da mai ido, na yadda matasa da daman gaske ke nisanta kan su daga shiga shaye-shaye, da akasarin matasa a baya suka runguma da hannu biyu, wanda ba karamin durkusar da rayuwar matasa shaye-shaye ke haifar wa ba.

Sauran nasarorin da Walin Fagachin Zazzau, Alhaji Salisu Abdu ya ce sun samu kuwa sun hada da ganin matasan jihar Kaduna sun sami shiga aikin soja , a wannan shekara ta 2018.Ya kara da cewar, matasan da suka sami shiga aikin sojan, sun fito ne daga kananan hukumomin jihar Kaduna.

A tsokacin da Walin Fagachin Zazzau ya yi kan wayar da kan matasa, na su nisanta kansu daga shiga shaye-shaye da kuma sauran muggan ayyuka, ya ce, sun shirya taron ilmatar da matasa illolin yin abubuwan da aka ambata.ya ce kungiyarsu, ta shirya taron ilmantar da matasan illolin abubuwan da aka ambata a kananan hukumomin Kaciya da Kaura da Kajuru da Soba da Giwa da Makarfi da Jema’a da Igabi da Ikara da Lere da Sabon gari da kuma karamar hukumar Zariya.

Domin ci gaba da kula da tarbiyyar matasa kuwa, Walin Fagachin Zazzau, Alhaji Salisu Abdu, ya yi kira ga iyayen yara da su kara tashi tsaye na ganin yaransu sun daina shaye-shaye da kuma sauran muggan ayyuka da a yau, wasu matasan suka runguma dare-da-rana.

Walin Fagachin Zazzau, ya kammala da yaba wa gwamnatin jihar Kaduna, na yadda ta samar da wasu kafafe da suke tallafa wa rayuwar matasa,kamar aikin hukumar KASTELEA da share hanyoyi da ake yi da kuma yadda ta kada kugen daukar sabbin malamai a daukacin kananan hukumomin jihar Kaduna 23.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai