Connect with us

LABARAI

Magu Zai Shugabanci Taron Kungiyoyin Yaki Da Cin Hanci Na Kasashen Afrika Renon Ingila

Published

on


An nada Mukaddashin shugaban hukumar yaki da abubuwan da kan karya tattalin arzikin kasa, EFCC, Ibrahim Magu, a matsayin sabon shugaban hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afrika, renon Ingila.

Hakan ya biyo bayan sanarwar bayan taro ne da aka bayar a karshen taron kwanaki biyar da aka yi a Abuja, jiya.

Hakanan taron ya jaddada bukatar samar da hadin kai da taimakon juna a tsakanin kasashen da ke cikin kungiyar da nufin ganowa da kuma kwato dukiyoyin haramun.

Taron mai taken, “Partnering Towards Assets Recobery and Return”  da sauran su, ya nu na damuwarsa kan irin hasarar da kasashen na Afrika ke tafkawa a sakamakon kai komon kudi ta hanyar haramun, inda taron ya bayar da shawarar samar da hadin kai na musamman a tsakanin kasashen da ke cikin kungiyar domin dakile cuwa-cuwar da ake tafkawa.

Taron kuma ya yi kira ga sassan shari’a da su bayar da hadin kai wajen magance matsalolin na almundahana.

Taron kuma ya karfafi dukkanin kungiyoyi da hukumomin na Afrika da su samar da wasu hanyoyi na wayar da kai da ilmantar wa ga al’umma kan mahimmancin sa hannun su wajen gano dukiyoyi da kadarorin  haramun.

Taron ya yaba da ayyukan da hukumonin yaki da almundahanan na Nijeriya kamar su EFCC da NCPC da ma al’umman Nijeriya suke yi, inda taron ya yaba da kasancewar Shugaba Buhari a wajen taron wanda mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilce shi a wajen bude taron.

A sa’ilin kuma da taron ya yaba da hada hannun daukan nauyin taron, ya kuma yaba da kokarin babban Sakataren kungiyar kasashen na Afrika renon Ingila, Baroness Patricia Scotland; tsaffin shugabannin kasa, Janaral Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar; tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Thambo Mbeki, da kuma marubucin nan,Farfesa Wole Soyinka, a wajen taron.

kasashe 19 ne da suka hada da Nijeriya suka halarci taron.

Kasar Uganda ne tare da hadin gwiwar sakatariyar kasashen na Afrika renon Ingila za su dauki nauyin taro na gaba wanda za a yi a kasar ta Uganda.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai