Connect with us

LABARAI

Lalata Bututun Mai: An Kama Sama Da Jarkuna 500 A Legas Da Ogun

Published

on


Jami’an tsaro a karshen makon nan a Jihohin Legas da Ogun, sun kama sama da Jarkuna 500 shaqe da Man fetur da kuma motoci 28.
Hakanan, sun kama mutanen da ake zargi 17, da Sojojin qarya 12 gami da ‘yan qungiyar asiri 11 a wurare daban-daban na Jihohin Legas da Ogun.
Hakanan kuma a wani farmakin da jami’an tsaron suka kai, a yankin Akute na Jihar Ogun, sun damqe sama da jarkuna 400 shaqe da man na fetur, da kuma wani bututun janyo man mai tsawon kimanin mita 500 da kuma wasu kayan aikin vatagarin.
Kwamandan rundunar ta 81, Manjo Janar Enobong Udoh, a sa’ilin da yake nu na wa manema labarai mutanan da suka kama, ya ce Sojoji za su ci gaba da sanya hannu wajen kare dukiyar qasarnan, don haka sai ya nemi qarin hadin kan al’umma.


Advertisement
Click to comment

labarai