Connect with us

LABARAI

Kwalejin Gwamnatin Tarayya Dake Bauchi Zai Fara Koyar Da Digiri A Fannoni Biyar

Published

on


Shirye-shiryen hadaka a tsakanin Jami’ar ABU da Kwalejin gwamnatin tarayya da ke Bauchi na fara koyar da ilimi mai zurfi a matakin digiri kan kwasa-kwasai biyar ya yi nisa.

Kwasa-kwasan su ne ilimin aikin jarida, fannin hidimar kiddiga da kuma hada-hadar kudi, sashin koyon ilimin gudanar da mulki, harkar kasuwanci da kuma gudanarwa, sai kuma karshe ilimin kidaya.

Hakan na daga cikin bukatar da kwalejin ta tura na yin hadaka da wasu Jami’o’in kasar nan domin fara koyar da digiri ne, inda Jami’ar Ahmadu Bello Unibersity, Zaria ta turo jami’anta domin su binciko musu kayyaki da kuma ababen da kwalejin kimiyya ta jihar Bauchi ke da su domin ganin yadda za su yi wajen fara hadaka don koyar da ilimi a matakin digiri.

Tawagar jami’ar ta ABU mai mutane takwas, ta je kwalejin ne a makon jiya domin duba kayyaki, ma’aikata, dakunan adana kayyakin tarihi da kuma gine-ginen da za koyar da digiri din.

Shugaban kwalejin ta Federal Poly Bauchi Arc. Sanusi Waziri Gumau shi ya fara tarban kwamitin gabanin zagayawa da su domin ganewa da idonsu kan ababen da kwalejin ke da su a kasa.

Da yake jawabinsa bayan kammala duba yanayin cikin kwalejin, jagoran tawagar jami’an ABU Farfesa Sa’ad A. Ahmed ya nuna matukar gamsuwarsa da irin ababen da suka riska a cikin kwalejin kimiyya ta Bauchi.

Farfesan ya bayyana cewar kayyakin makarantar, gine-gine, dakunan bincike da nazarin karatu, kwarewar ma’aikata, kayyakin da suka kunshi hidimar wassani da kuma dakunan na’urar yanar gizo (ICT) na kwajejin dukkaninsu ya nuna gamsuwar a bisa yadda ya samesu, yana mai kiran hukumar gudanarwa da ta ci gaba da sanya kula da lura a kan kayyakin.

Farfesa Sa’ad Ahmed wanda kuma har-ila-yau, shi ne mataimakin Daktan tsare-tsare na jami’ar ABU Zariya, ya bayyana cewar dukkanin matakan da suka kamata su bi a tsakanin kwalejin da jami’ar na fara koyar da digiri sun yi nisa, yana mai bayanin cewar nan gaba kadan za su fara aiwatar da kwasa-kwasai da suka kulla yarjejeniya a kansu.

Da yake maida jawabinsa, shugaban kwalejin kimiyya, fasaha da kuma kere-kere na gwamnatin tarayya da ke Bauchi Arc. Sanusi Waziri Gumau ya nuna godiyarsa ne ga jami’ar ta ABU a bisa turo tawaga domin bincike hade da duba ababen da kwalejin ke da su domin fara aiwatar da yarjejeniyar da suke a tsakani.

Arc. Gumau ya bayyana cewar wannan matakin zai kawo wa kwalejin ci gaba gagaruma, yana mai bayanin cewar za kuma su ci gaba da zage damtse wajen kyautata kwalejin ya kuma shaida cewar dukkanin daliban da za a fara wadannan kwasa-kwasai da su za su samu nagartaccen ilimi.

LEADERSHIP A Yau ta labarto cewar Fannonin da kwalejin za ta fara koyar da digiri a kansu sun hada da sashin nazarin ilimin aikin jarida wato (Mass Communication)  hidimar kiddiga da kuma hada-hadar kudi (Accountancy) sashin koyon ilimin gudanar da mulki  (Public Administration) harkar kasuwanci da kuma gudanarwa (Business Administration and Management) sai kuma karshe  ilimin kidaya  (Statistics).


Advertisement
Click to comment

labarai