Connect with us

LABARAI

Kungiyar Masu Hada Magunguna Ta Fara Janye Kodin Daga Kasuwa

Published

on


Kungiyar kamfanonin da ke hada magunguna ta kasa, ta fara janye maganin tari na ruwan Kodin daga kasuwa domin cika umurnin gwamnati kan hakan.

Magatakardan knngiyar ne, Elijah Mohammed, ya sanar da hakan cikin wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Asabar a Abuja.

Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ne ya umurci kungiyar ta PCN da hukumar NAFDAC da sauran masu hannu cikin lamarin da su hanzarta janye maganin na Kodin daga kasuwa.

Mista Mohammed ya kara tabbatar da cewa, Kodin sinadari ne mai kama da morphine, wanda aka yarda da shi ake kuma iya samun sa a dukkanin wuraren sayar da magunguna, wanda idan aka sha kadan din shi zai saukaka wa masu fama da ciwon tari.

“Sai dai kuma, sakamakon abubuwan da ke cikin sa, idan aka kwankwade shi na tsawon zamani zai iya haifar da wata matsalar ta daban.

Ya ce, a bisa bin umurnin Ministan, kungiyar na su tuni ta fara aiwatar da shirin na janye maganin na Kodin daga Jihohin Ogun, Sakkwato da Jihar Nassarawa, ya kara da cewa a yanzun haka su na gudanar da shirin hakan a Jihar Adamawa.

Mista Mohammed, wanda ya nanata cewa, Kodin ba shi cikin maganukan da hukumar tantancewa ta PPMB ta yarje wa, ya gargade su da su guji sayar da maganin tarin na Kodin da sauran magunukan da ba a tantance su ba don gujewa takunkumi.

A cewar shi, bisa kokarin kungiyar na su na raba al’umma da maganin tarin na Kodin, sun yi zama da shugabannin kungiyar, ACPN, na kasa, inda duk suka dauki alkawarin hada hannu wajen janye Kodin din daga kasuwa.

Sai dai, Mista Mohammed, ya yi roko ga kamfanonin da ke hada magungunan da masu shigowa da su da masu raba su da su sanya tsoron Allah wajen bin dokar ta hanin tu’ammuli da Kodin din.

“Ka da son dukiya da abin duniya ya rinjayi kare lafiyarmu mai dangantaka da shan maganin ba bisa ka’ida ba.

“Mu saka lafiyar ‘yan Nijeriya a gaba da komai.

A ranar 1 ga watan Mayu ne gwamnatin tarayya ta yi hani da yin maganin tarin na Kodin, ko shigowa da shi ko kuma sayar da shi a cikin kasarnan.

Gwamnatin kuma ta umurci hukumar ta NAFDAC da ta daina bayar da lasisin shigowa da sinadarin na Kodin wanda ake hada maganin tarin da shi.

Hakanan kuma, ta umurci hukumar ta PCN da NAFDAC, da su sanya ido wajen ganin lallai an janye maganin tarin daga dukkanin kasuwannin kasarnan.

Bayar da wannan umurnin ya zama wajibi sakamakon yadda ake tu’ammuli da maganin tarin na Kodin ba bisa ka’ida ba a cikin kasarnan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai