Connect with us

LABARAI

Jam’iyyar APC A Jihar Borno Ta Nuna Amincewarta Da Gwamnatin Shettima

Published

on


Dukkanin wakilan da suka halarci babban taron da Jam’iyyar APC ta yi a Jihar Borno, sun nu na amincewar su da salon jagorancin Gwamna Kashim Shettima a Jihar.

Jiga-jigan Jam’iyyar da suka fito daga sassan mazabun kananan hukumomi 27 na Jihar, sun yi nu ni da namijin kokarin da Gwamna Kashim ya yi a fannin aiwatar da manyan ayyuka, Ilimi, daukan nauyin ‘yan gudun hijira yadda ya dace da sauran su, inda suka ce ya sami duk wannan nasarar ne duk kuwa da baranazar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Da yake nu na bukatar neman amincewar taron kan gwamnatain ta Gwamna Kashim, a cibiyar wasanni ta Elkanemi Warriors, da ke Maiduguri, Kwamishinan Ilimi mai zurfi, kuma wakili daga Karamar Hukumar Gwoza, Honorabul Ahmed Babab Jaha, (Babawo), ya bayyana Gwamna Shettima, a matsayin wata kyauta ce daga Allah ga al’ummar Jihar.

Honorabul Abba Jato Muhammed, wakili daga karamar hukumar Bama ne ya goyi bayan bukatar hakan.

Daga nan ne sai daukacin wakilan suka amsa bakidayansu da cewa, “mun goyi baya.”

An dai dinke cibiyar wasannin ta Elkanemi Warriors da jami’an tsaro na ‘yan sanda da na farin kaya domin a tabbatar da an yi taron lafiya.

Hakanan an hana ‘yan bangan siyasa daga shiga filin taron, wanda hakan ya sanya taron na wadanda aka gayyata ne kadai.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai