Connect with us

LABARAI

Hajiya Hafsat Ganduje Ta Rabawa Mata 200 Jari Domin Dogaro Da Kai

Published

on


Mai Dakin Gwamnan Kanno Hajiya Hafsat Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta sake rabawa mata 200 Jari a Karamar Hukumar Hukumar Ajingi, Kamar yadda aka sani yana da cikin manyan kudurorin Gwamnatin Ganduje inganta rayuwar al’ummar tare da samar da tsarin dogaro da kai. Wannan Gwamnatin Kano ta karkashin Mai Dakin Gwamnan na Kano Hajiya Hafsat Ganduje  ta kuduir aniyar  inganta rayuwar al’umma  ta hanyar koyawa mata sana’un da zasu dogara da kansu.

Hajiya Hafsat Ganduje ta tabbatarwa wadannan mata 200  daga karamar Hukumar Ajingi cewar  kowacce mace guda zata karbi Naira dubu goma domin zama Jari wajen gudanar da kananan sana’un da suka koya,  Wannan na cikin kyakkayawan aniyar Gwamnatin Ganduje na kyautatawa Matan karkara dana birane. Saboda Haka sai Mai dakin Gwamna ta hori wadanda suka amfana da wannan kabakin arziki da cewar suyi kyakkyawan amfani das hi.

Idan za’a iya tunawa gwamnatin Kano ta daga likkafar dubban matasa  maza da mata, misali  mata 5,200 wanda akoyawa sana’u iri daban daban,  Samari masu sana’ar sayar da Shayi guda  5,200,  masu tukin adaidata sahu 2,500 tare da gina cibiyar koyar da sana’u iri daban daban  wadda nan bada jimawa za’a budeta. Don haka sai mai dakin na Gwamna ta ja kunnen wadanda aka baiwa wannan tallafi dasu kara hakurin ci gaba kula da gidajen mazajensu.

Hakazalika Hajiya Hafsata Ganduje ta ja kunnen mata wajen lura da yaransu don kare su daga annobar shaye shaye wadda wannan matsalace babba, sannan kuma ta bukaci iyaye da suyi kokari shigar da yaran su makaranta ba tare da ware mace ko namiji ba. Ta kuma bayyana amfanin ilimin ‘ya mace.


Advertisement
Click to comment

labarai