Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Ta Biya ’Yan Fansho Naira Bilyan 23 A Watanni Uku

Published

on


Kimanin Naira bilyan 22.45 ne gwamnatin tarayya ta biya masu karban kudin Fansho a karkashin wani shirin biyan hakkoki na musamman a tsakanin watannin Janairu da kuma Maris na wannan shekarar.

Wadannan alkaluma da suka fito daga hukumar ta ce, sunayen ‘yan Fanshon na hakika a ranar Juma’a, sun nu na cewa, an biya ‘yan Fanshon kudaden ne bayan da aka tantance na gaskiyan daga cikinsu.

Alkaluman sun nuna an biya Naira bilyan 6.66 ne ga wadanda suka ajiye aiki a ma’aikatun gwamnati, inda kuma aka biya Naira bilyan 12 ga wadanda suka ajiye aiki a wasu hukumomi na gwamnati, inda kuma aka biya wadanda suka ajiye ayyuka daga hukumomin Kwastam da jami’an shige da fice Naira bilyan 1.86, masu karban kudaden Fanshon daga hukumar ‘yan sanda sun sami Naira bilyan 1.68.

Tsarin biyan kudaden ya nu na an biya Naira bilyan 2.21 ne a watan Janairu, ga ma’aikatan gwamnati 111,525, su kuma, manyan Sakatarorin ma’aikatun gwamnati da shugabannin ma’aikatu da suka yi ritaya su 219, an biya su Naira bilyan 2.2 a watan na Fabrairu. A watan Maris kuma an biya ma’aikatan gwamnat da manyan sakatarorin Naira bilyan 2.2.

Ga ma’aikatan gwamnatin da ke karkashin shirin biyan hakkokin na musamman an biya su Naira bilyan 2.12 ga masu karban Fansho 111,525, a watan Janairu, a watan Fabrairu da Maris kuma an biya su Naira bilyan 2.21 da kuma Naira bilyan 2.2 bi da bi.

Da take magana kan wannan ci gaban da aka samu, babbar sakatariyar hukumar biyan kudaden na Fansho, Sharon Ikeazor, ta ce, ya zuwa yanzun gwamnatin tarayya ba ta iya biyan kashi 33 na kudaden ariyan ‘yan Fanshon ba na watanni 12, inda su kuwa ma’aikatan hukumomin gwamnati ke bin bashin ariyan na tsakanin watanni 18 zuwa 36, ‘yan sanda kuma su na bin bashin na watanni 12 ne.

Ta ce, hukumar na su tana yin duk abin da ya kamata na ganin ta biya wadannan basukan, inda ta kara da cewa ariyan na wasu sassan jami’an tsaro su duk an kammala biyan su bakidaya.

Ikeazor ta ce, ta dakatar da biyan wasu masu karban Fanshon su 19,000 wadanda suke da matsala lambobin su na tantancewa a Bankuna da suka saba da abin ke cikin takardun da ake biyan su kudi.

Ta ce dukkanin masu karban Fanshon da aka dakatar da kudaden na su, za a sake mayar da biyan su kudaden ne in sun gyara matsalar na su na, ‘BBN.’

Ta kuma ce za su ci gaba da tantancewa domin gano masu karban Fanshon bogi ta na’urorin su.

Ikeazor ta ce, baya ga ‘yan Fansho 19,000 da suke da matsalar ta , ‘BBN,’ an kuma dakatar da biyan kudaden na su, akwai kuma wasu 22,021 da su ma an dakatar da biyan su domin sun kasa su nu na kansu a lokutan da aka gudanar da tantancewa a fadin kasarnan.

Ta ce kuma sun sami nasarar tantancewa da kuma kara ‘yan Fansho 7,969 a kan takardun biyan kudin. ta ce sun kuma fito ne daga Kudu maso Yammaci da kuma Arewa ta tsakiya a kwata na 4 na 2017.

“Kafin mu yi wannan karin, sama da ‘yan Fansho 19500 da muka tantance ne da suka fito daga Arewa maso Yamma, Kudu maso Gabas, Arewa maso Gabas da kuma Kudu maso kudancin kasarnan duk an mayar da su ana kuma biya su kudaden ariyan su na Fansho din.

“Mun kuma kara masu karban Fanshon 700 da muka tantance daga hukumomin gwamnati na hukumar samar da gidaje ta tarayya a tsarin biyan kudin na Fansho.”

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai