Connect with us

LABARAI

Birnin Gwari: An Sace Matan Aure Uku A Kaduna

Published

on


A jiya ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata tsammanin barayin shanu ne sace wasu matan aure har guda uku kauyen Maganda dake Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Matan auren da aka sace sun kasance mata ne ga wani dan kasuwa mai suna Alhaji Adamu Nakwana dake kauyen Maganda ta karamar hukumar Birnin Gwarin.

Yayin da yake yin karin bayani ga kafar PRNigeria, wani babba a cikin ‘yan sintirin wannan yanki na Birnin Gwari, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa barayin shanun sun iso wannan kauye na Maganda ne cikin dare.

Dan Sintirin ya shaida cewa, “A yau Lahadi da misalin karfe 1:30 ne wasu barayin Shanu suka kaddamar da farmaki a kauyen Bagauda inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

“Daga nan ne suka kai sumame gidan Alhaji Adamu Nakwalla, inda suka sace matansa guda uku. Amma daga baya sun sako daya daga cikin matan, wacce kuma suka bata lambar waya wacce suka ce a neme su da ita.

“Dama tun kafin afkuwar lamarin, sai da barayin Shanun suka aiko da sakon gargadi ga al’ummar wannan kauye. inda suka bayyana cewa, suna nan zuwa. Sai dai cikin ikon Allah ba a samu salwantar rayuka ba. amma san samu wani bawan Allah wanda ya samu raunin harsashi.” Inji shi

Mazauna kauyen na Maganda wadanda suke kan babbar hanyar zuwa karamar hukumar Funtuwa dake cikin jihar Katsina sun yi ta gudun neman tsira a yayin da barayin shanun suka dira garin.

Rahotanni sun bayyana cewar, ‘yan bindigar kimanin su 80 sun yi wa kauyen kawanya ne tare da hana kowa fita lokacin da suka kai farmakin.

A wata sabuwa barayin shanu sun sake kaddamar da wani sabon hari a a Karamar Hukumar ta Birnin Gwari awanni kadan da sace wadannan matan aure.

A sabon harin ne suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da mutane shida a yankin. Sabuwar ta’asar ta auku ne da misalign karfe 9:00 na safiyar jiya Lahadi, bayan da yan bindigar suka bude wuta akan wata motar haya wacce ke dauke da wadanda lamarin ya rutsa dasu.

Budewa motar wuta ya janyo mutawar fasinja daya bayan da motar dake dauke da fasinjojin ta kwace wa direben ta nufi daji. Shugaban kungiyar Direbobi (NURTW)‎ dake  Birnin Gwari, Danladi Duniya ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Danladi Duniya ya ce, direban ya tuko motar ne mai kirar Bolkswagen Golf 3 ya samu ya arce a lokacin da aka tafi da sauran fasinjojinsa shida.

Ya kara da cewa, fasinjan da ya rasa ransa tuni an kai gawar sa kauyen Buruku inda aka bizne shi.

LEADERSHIP A Yau ta tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, ASP Mukhtar Aliyu don karin bayani, amma layin wayar sa ba ya tafiya har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 


Advertisement
Click to comment

labarai